Sanata mai wakiltar Kogi ta ya yi tir da karrama marigayi Abiola da shugaba Muhammadu Buhari yayi da lamabar girmamawa ta GCFR.
Ya ce bai ga dalilin da zai sa shugaba Buhari ya mika irin wannan babbar lambar yabo ga mutumin da bashi a duniya ba.
” Abiola ba dan Najeriya bane yanzu tunda ya riga ya rasu, ita kuma wannan lambar girmamawa a na ba rayayye ne kuma dan kasa. Haka take a doka amma ba wai don kawai ana so aburge ba sai a keta doka babu gaira babu dalili.
” Mutuwar Abiola kawai ya maida dashi ba dan Najeriya ba.
Dino ya ce tabbas idan har hakan zai zauna toh fa sai an yi wa dokar gyara.
Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya canza ranar murna da hutun dimokradiyya a kasar nan zuwa ranar 12 ga watan Yuni daga 2019.
Buhari yayi haka ne domin ya karrama marigayi Abiola da ake zaton shine ya lashe zaben 12 ga watan Yuli din da shugaban kasa a wancan lokacin Ibrahim Babangida ya soke zaben.
Bayan haka shugaba Buhari ya ce zai bai wa marigayi Abiola babbar lambar girmamawa ta GCFR wanda babu wanda yake samun wannan lambar girmamawa sai tsohon shugaban Kasa wanda hakan ya nuna kamar Abiola ma tsohon shugaban kasa ne.
Mataimakin Abiola a takarar wato Ambasada Babagana Kingibe shima za a bashi lambar girmamawa na GCON.