Duk wanda ya bi JOHESU yajin aiki ba za a biya shi albashi ba – Gwamnati

0

Gwamnatin tarayya ta sanar cewa ba za ta biya duk wani ma’aikacin asibiti da bai zo aiki albashi ba lokacin da kungiyar ma’aikatan asibitoci karkashin (JOHESU) suka shiga yajin aiki.

Idan ba a manta ba mako guda da fara yajin aiki gwamnatin ta yi wa kungiyar barazanar hana su albashi idan har ba su koma aiki ba.

A wancan lokacin JOHESU ta yi ‘Kunen Uwar Shegu’ da wannan barazana na gwamnati ta ci gaba da yajin aikin ta.

Ofishin ma’aikatar kiwon lafiya ta aika wa shugabanin asibitocin gwamnati dake kasar ranar Talata da su aika da sunayen duk ma’aikatan jinyar da suka zo aiki a lokacin da JOHESU ke yajin aiki.

Jami’in ma’aikatar O.J Amedu wanda ya sa hannu a wasikar ya bayyana cewa gwamnati ta yi haka ne domin ta san ma’aikatan da suka zo aiki domin a biya su albashin su.

Daga karshe shugaban babbar asibitin Abuja Jaf Momoh da shugaban asibitin koyarwa na jami’ar Calaba Thomas Agan sun tabbatar da samun wasikar sannan suna shirin aikawa ma’aikatar da sunayen ma’aikatan da suka zo aiki.

Sai dai shugaban asibitin koyarwa na jami’ar Legas Chris Bode ya ce yana da masaniya kan wasikar amma har yanzu bai ga wasikar da idanunsa.

Shugaban kungiyar JOHESU Biobelemoye Josiah da mataimakinsa Ogbonna Chimela basu ce komai ba game da wannan batu.

Share.

game da Author