Kokarin Jolly Nyame na neman beli daga kurkuku ya ci tura

0

Mai Shari’a Adebukola Bankojo ta Babbar Kotun Abuja, ta yi watsi ta neman beli daga kurkuku da lauyan tsohon gwamnan jihar Taraba, Jolly Nyame ya shigar a madadin sa.

Dama da ita Banjoko din ce ta dauke Nyame shekaru 14 a gidan kurkuku a ranar 14 Ga Mayu na wannan shekara.

Lauya Olalekan Ojo, ya garzaya kotun ranar Laraba, ya na neman a ba shi belin bisa dalilin cewa Nyame ya na fama da ciwon hawan-jini da kuma ciwon-suga.

Ya ce don haka akwai bukatar gaggawa ta neman maganin gargajiya da kuma kulawa da ake yi da shi ta hanyar maganin gargajiya shekara da shekaru.

“Ya Mai Shari’a, wanda na ke karewa ya na fama da wannan matsanancin hali tun shekaru goma da suka gabata, ya nemi umarni daga jami’an gidan kurkukun Kuje na su bar shi a rika yi masa amfani da maganin san a gargajiya, amma ba su yarda ba.” Haka Ojo lauyan Nyame ya shaida wa kotu jiya Laraba.

Ya kara da bayyana wa kotun cewa ranar 19 Ga Yuni, Babban Asibitin jihar Taraba ya bayar da sakamakon binciken da suka yi a kan Nyame, inda ya ce bincike ya tabbatar da cewa, idan ba a fito da shi daga kurkuku ba, to zai nan ba da dadewa ba zai iya rasa ran sa.

Daga nan sai lauyan ya gabatar wa kotu takardun sakamakon binciken domin mai shari’a ta tabbatar.

Shi kuma lauyan EFCC, Rotimi Jacobs, ya ki amincewa da rokon da lauyan Nyame ya yi.

Ita ma Mai Shari’a ba ta amince ba, a bisa dalilin cewa akwai alamomin tambaya a kan bambancin ranar da aka fito da sakamakon gwajin daga asibitin Taraba.

Daga nan sai ta ce Ma’aikatar Harkokin Cikin Gida ce lauyan zai rubuta wa wasika ya nemi iznin bayar da maganin gargajiya ga tsohon gwamnan. Ta ce kurkukun ya ki yarda ne saboda ba zaman kan sa ya ke yi ba, ya na a karkashin ma’aikatar ne.

Share.

game da Author