Sojoji sun kashe Boko Haram shida, sun ceto mutane 33

0

Sojojin Najeriya sun kashe ‘yan Boko Haram shida tare da ceto mutane 33 a cikin dajin Barno.

An kakkabe Boko Haram din ne da cikin dazukan Damboa da Bama, cikin jihar Barno.

Wadanda aka ceto din sun hada da maza takwas, mata 12, kananan yara 13.

Kakakin yada labaran sojoji Texax Chukwu ne ya bayyana haka a cikin wata takardar manema labarai da ya fitar.

Ya ce ana ci gaba da tantance wadanda aka ceto din, kuma da zaran an kammala, za a damka su ga hukumar da ta dace domin kulawa da su.

Ya kara da cewa an kwato bindiga samfurin AK 47 har guda shida a hannun Boko Haram.

Chukwu ya kara da cewa an samu kananan bindigogi, albarusai, gurneti da nakiyoyi a hannun Boko Haram din.

An kuma samu kakin sojoji har uku da kuma da wasu makaman a hannun su.

Share.

game da Author