Kungiyar kula da kiwon lafiya ta duniya (WHO) ta sanar cewa ta hana wani magani mai suna ‘Carbetocin’ dake da ingancin kare mata fadawa matsalar zuban jini bayan sun haihu.
WHO ta bayyana cewa yawan zuban jini matsala ce da mata kan yi fama da shi bayan sun haihu sannan idan ba a gaggauta daukan mataki ba yakan yi ajalin su.
” Bayanan wani bincike ya nuna cewa a duk shekara matan dake fadawa irin wannan matsalar a duniya sun kai 70,000. Kuma ya nuna cewa jariran da wadannan mata ke haihuwa kan rasu cikin wata daya bayan an haife su saboda rashin uwayen su.
A tsokacin da ya yi shugaban kungiyar WHO Tedros Adhanom Ghebreyesus ya bayyana cewa domin kawar da irin haka ne ya sa suka fara sarrafa maganin ‘Oxytocin’.
” Sai dai babbar matsalar da muke fama da wannan maganin shine ajiye maganin a wuri mai sanyi a kowani lokaci.
Ghebreyesus yace ganin irin wannan matsalar da suke fama da su na wurin ajiya mai sanyi ne ya sa suka kara sarrafa wani maganin mai suna ‘Carbetocin’ da ba sai dole an ajiye shi a wurin da ke da sanyi ba.
” Samun wannan maganin ya tabbatar mana da cewa za mu iya ceto rayukan mata musamman na kasashen dake tasowa sannan suna fama da wannan matsala.
Discussion about this post