Dakarun soji sun kashe Boko Haram 23 a kauyukan Chadi

0

Jami’in yada labarai na dakarun sojin Najeriya Texas Chukwu ya bayyana cewa rundunar bataliyan 153 tare da hadin gwiwar sojojin kasar Kamaru sun kashe wasu ‘yan Boko Haram 23 a wasu kayukan tafkin Chadi.

Ya bayyana haka ne ranar Talata a Maiduguri inda ya kara da cewa da yawan ‘yan Boko Haram din sun gudu da raunin harsashi a jikin su.

Ya ce sun kwashi makamai da dama tare da baburan hawa biyu daga mabuyar Boko Haram din.

Bayan haka kuma dakarun sojin sun kuma fatattaki Boko Haram daga kauyukan Bulakeisa, Tumbuma Babba, Abbaganaram da Dan Baure duk a tsibirin tafkin Chadi.

Share.

game da Author