Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Anambara Haruna Umar ya bayyana cewa ma’aikatan rundunar sa sun kubutar da wani shugaban makarantar sakandare ‘Wisdom Secondary School’ dake kauyen Okija a karamar hukumar Ihaila daga fushin matasan kauyen da suka nemi ganin bayan sa.
Matasan kauyen Okija sun far wa wannan shugaban makaranta ne mai suna Modestus Eze bayan zargin sa da suke yi da aikata fasikanci da wani matashi dan shekara 17 a makarantar sa.
Umar ya ce sun gaggauta zuwa makarantar ne bayan sun ji kishin-kishin din harin da wadannan matasa suka so yi wa wannan shugaban makaranta.
” Matasan sun bayyana mana cewa suna da labarin cewa wannan ba shine karo na farkon da shugaban makarantar yake aikata hakan ba da ‘ya’yan mutane.
Umar ya ce sun gano wasu komatsai, jini da wasu tkarikitan tsafe-tsafe a cikin wasu ajujuwan makarantan.
” Sai dai shugaban makaranta wato Modestus Eze ya sulale daga hannun mu kafin mu sami damar yi masa tambayoyi.”
A karshe yace tuni an baza ‘yan sanda sa jami’an sirri domin zakulo wannan hatsabibin mutum domin hukunta shi.
Discussion about this post