MURNA TA KOMA CIKI: An hana Morocco daukar nauyin gasar Cin Kofin Duniya na 2026

0

Taron Majalisar Koli na Kungiyar Kwallon Kafa ta Duniya (FIFA), ya amince da kasashen Amurka, Canada da Mexico su dauki nauyin hadin guiwar gasar Cin Kofin Duniya na shekarar 2026.

An yi zabe ne ida gamayyar kasashen suka samu kuri’u sama da kasar Morocco, wadda ta sa rai sosai za ta samu nasarar daukar nauyin gasar.

An gudanar da zaben ne a Cibiyar Expocentre da ke birnin Moscow, babban birnin kasar Rasha, inda za a fara fafata gasar cin kofin na duniya na 2018, nan da kwanaki biyu.

Shugaban FIFA Gianni Infantino ne ya bayyana sakamakon zaben.

Yayin da Morocco ta samu kuri’a 63, gamayyar kasashen Amurka, Canada da Mexico kuma sun samu kuri’u 134.

Sai dai kuma wani karin haske da aka nuna, shi ne, Morocco na bukatar karin gina filayen wasa na zamani har guda 9, kasancewa a gasa ta 2026 za a yi amfani da kungiyoyin kwallo daga kasashe 48 ne.

An tabbatar da cewa kasashen uku wato Amurka da Canada da kuma Mexico, duk su na da wadatar filayen wasan da ake bukata.

Hakan ne ya sa ake ganin cewa gudanar da gasar a wadannan kasashe, ba ta da bukatar kara kashe wasu dimbin makudan kudade, kamar inda a kasar Morocco ne za a gudanar da gasar.

Kalubalen kawai da za a fuskanta a gasar da za a yi a kasashen uku, ita ce karakainar kungiyoyi daga wannan kasa zuwa waccan idan aka fara gasar.

Wannan kuwa ana ganin ba zai kawo bata lokaci ko wani cikas ba, kasancewa tsarin zirga-zirga na zamani zai magance komai, kuma zai hana kawo duk wani tsaicon da ake hangen ka iya faruwa.

Share.

game da Author