ZABEN KADUNA: Mutane ba su fito zabe ba

0

A yaune jihar Kaduna ke gudanar da zabukan kananan hukumomi da na kansiloli a fadin Jihar. Sai dai abin takaici da ban haushi shine ganin yadda har zuwa karfe dayan rana wasu mazabun basu ji kamshin isowar jami’an zabe ba ballantana su kada kuri’un su.

Har yanzu shiru kake ji awasu mazabun, inda a wasu kuma an riga da har an yi zabe.

Wakilin PREMIUM TIMES HAUSA ya zazzagaya wasu rumfunar zabe a jihar inda ya ga kwayoyin mutane suna kan layi domin kada kuri’ar su.

A wasu rumfunar zaben kuwa a unguwannin Barnawa, Kakuri,Tudun Wada, Rigasa, Unguwan shanu, Nasarawa, Rafin Guza, duk har yanzu ba a ma kawo na’aurar zaben ba.

Yakubu Aliyu, mazaunin unguwar Maiduguri road, ya shaida mana cewa, a unguwar su jami’an zabe sun iso har wasu ma sun kammala zabe.

” A wannan unguwa dai, an yi zabe, sai dai mutane ne basu fito sun kada kuri’a ba sosai.
sannan kuma wasu wuraren ba a ma kawo akwatunan zaben ba.

Shiko Hassan Mohammed, cewa yayi, haryanzu ba akawo akwatunan zabe ba a rumfunan da ke unguwannin su a karamar Hukumar Lere ba.

A nashi tsokaci, wani jigo a jam’iyyar PDP, sannan tsohon kakakin tsohon gwamnan jihar Kaduna Ramalan Yero, Ahmed Maiyaki cewa yayi tabbas, gwamnatin Kaduna bata shirya wa wannan zabe ba.

Ya ce gwamnatin jihar karkashin jagorancin gwamna El-Rufai yaudaran mutane kawai suke yi amma ba da gaske suke ba na wai za su yi adalci.

” Ina nan muna kula da yadda zabukan ke wakana, tabbas ba a zabe a wurare da yawa sannan shi wannan na’ura babu yadda za ayi a hana coge. shiri ne kawai don dole sai anyi amfani da abin da za a cuci mutane.

” Rahotannin da ya iske mu zuwa yanzu, har tafiya da na’urar zaben an ce anyi a karamar hukumar Igabi. Mu dai bamu yarda da wannan abu da akeyi na yi mana karfa-karfa a wannan zabe sannan za mu ci gaba da sa ido muga yadda tuyar wainar za ta kasance a karshe.

Share.

game da Author