Wani Magidanci ya bayyana wa kotu cewa garin neman asirin mallake shi ne matarsa ta fada hannu wasu bokayen suka ta yin lalata da ita.
Mijin nata mai suna Kehinde, ya bayyana wa kotu cewa a dalilin haka ne ya ke neman kotu ta raba auren sa da matar tasa domin ba zai iya zama da ita ba.
” Matata tana da burin gaske, da son duniya. Garin neman asirin mallake ni ne wasu malaman karya suka yi ta lalata da ita. Gashi yanzu bata ga tsuntsu bata ga tarko.”
Ya roki kotu da ta warware wannan aure domin abin ya ishe shi.
Da take fadin nata bayanin, matar Kehinde tace ita ma auren ya ishe ta hakanan. Ba za ta iya ci gaba da jure dukan da take sha ba a wurin mijin nata.
Da Alkalin kotun ya saurare su duka sai ya ce kotu ta amince ta warware auren cewa alamu ya nuna lallai basu kaunar ci gaba da zama da juna yanzu.