Duk Wanda Ya Rike Al-Qur’ani, Ba Zai Taba Tozarta Ba, Ba Zai Wulakanta Ba, Kuma Ba zai Tsiyace Ba, Daga Imam Murtadha Gusau

0

Bismillahir Rahmanir Rahim

Assalamu Alaikum

‘Yan uwa masu daraja. Hakika babu wata babbar ni’ima da Allah ya yiwa wannan al’ummah bayan ni’imar aiko da Annabi Muhammad (SAW) kamar bamu Alqur’ani mai girma. Mu rike Alqur’ani domin riko da shi alkhairi ne duniya da lahira.

Allah ya saukar da Alqur’ani ta hanyar daya daga cikin Mala’iku, wato Mala’ika Jibrilu zuwa ga Annabi Muhammad (SAW).

Sanadiyyar haka, sai Mala’ika Jibril ya zama mafi alkhairi, kuma mafi falala da matsayi a cikin sauran Mala’iku, saboda falalar saukar da Alqur’anin ta wajen sa shi kadai.

Kuma Allah ya saukar da Alqur’ani mai girma a cikin watan Ramadan, sai watan Ramadan ya zamanto wata mafi girman alkhairi da falala a kan sauran watannin shekara baki daya.

Shiyasa Allah ya shar’anta mana yin azumi a wannan watan saboda falalar saukar da alqur’ani a cikin sa.

An saukar da Alqur’ani a cikin daren Lailatul Qadri, sai daren ya kasance mafi alkhairin dare a cikin sauran dararen shekara baki daya, saboda albarkacin saukar da alkhairi da a kayi a cikin sa.

An saukar da Alqur’ani mai girma ga Annabi mafi girma Annabi Muhammad (SAW). Sai Annabi (SAW) ya zama mafi alkhairi da falala a kan sauran dukkanin Manzannin Allah baki daya.

An saukar da Alqur’ani ga wannan al’ummar ta Annabi Muhammad (SAW), sai sanadiyyar hakan ta zama mafi alkhairi da falala a kan sauran dukkan al’ummah baki daya, saboda falalar saukar da Alqur’ani mai girma a cikin ta.

Haka abun yake, da zan yi ta lissafi za ku ga cewa duk wani abinda yake da alaka da Alqur’ani, toh tabbas zai daukaka, zai yi albarka, zai yi daraja kuma falalar sa za ta yawaita.

Wallahi babu wanda zai girmama Alqur’ani face shima sai Allah ya girmama shi.

Mallam idan kana son daukakar duniya da lahira, ka zamanto mai hidima ga Alqur’ani da ma’abota Alqur’ani.

Idan kana son ka buwayi dukkan wani shedani, da dukkan wani marar kunya, da dukkan wani tsagera, toh rike Alqur’ani. Idan kana son kudi da dukiya mai albarka, rike Alqur’ani. Idan kana son mulki kuma mulkin ya zamanto mai albarka, rike Alqur’ani. Idan kana son zuri’ah da ‘ya ‘ya masu albarka, rike Alqur’ani. Idan kai mai sarauta ne, kuma kana son daukaka a sarautar ka, rike Alqur’ani. Idan kai Dan siyasa ne kana son daukaka a siyasar ka, rike Alqur’ani. Idan kuna son zaman lafiya, hadin kai, ci gaba, gyaruwar tattalin arziki, ku rike Alqur’ani. Idan kai Dan kasuwa ne, kuma kana son daukaka da albarka a kasuwancin ka, rike Alqur’ani. Idan kai ma’aikaci ne, kuma kana son daukaka a cikin aikin ka, toh rike Alqur’ani. Idan kai malamin Addini ne, yi kokarin aiki da abinda kake karantawa na Alqur’ani, za ka sha mamaki. Haka nan ma idan kai Dan boko ne, kuma kana son karin albarka da ci gaba a cikin bokon ka, toh rike Alqur’ani.

Ku zamanto masu yawan karatun Alqur’ani da kuma aiki da abinda kuke karatawa. Ku zamanto masu hidima ga Alqur’ani da ma’abota Alqur’anin. Da yardar Allah za ku ga ikon Allah. Za ku ga mu’ujizar Alqur’ani a cikin rayuwar ku da dukkanin al’amurran ku.

Wallahi, ku sani, duk rikice-rikice, da tashe-tashen hankula, da zubar da jini, da dimuwa da ake ciki yau a duniya, da rashin tabbas, da zaluntar marasa karfi da masu karfi suke yi, da fitin-tinu da musibu da bala’o’in da suke addabar duniya, sanadiyyar su shine barin Alqur’ani da tafarkin Manzon Allah (SAW).

Wallahi, Alqur’ani waraka ne, magani ne na ko wace irin cuta da ke damun ‘yan Adam.

Wallahi babu wani mutum da Alqur’ani zai sauka a zuciyar sa face ya wayi gari ya zama mafi alkhairin mutane, mafi daraja da daukakar mutane, sanadiyyar saukar Alqur’anin a zuciyar sa.

Shi yasa Manzon Allah (SAW) yake cewa:

“Mafi alkhairi a cikin ku shine wanda ya koyi Alqur’ani kuma yake koyar da shi.”

Kuma mafi hanyar godewa Allah akan ni’imar Alqur’ani a gare mu shine: Yin imani da shi a kan cewa magana ce ta Allah, kuma siffar Allah ne, ba Halittar Allah ba.

Kuma kayi imani da cewa, Alqur’ani shine littafin Allah na karshe wanda ya shafe sauran dukkanin littafai baki daya.

Kuma ka zamanto mai kokarin koyon karatun Alqur’ani da sanin ma’anonin sa da aiki dashi.

Kuma ka zamanto mai kokarin koyar da shi da yada shi, ko kuma ka zamanto mai taimakawa masu koyar da shi.

Ya kai Dan uwa, kar ka yarda ka yanke wa kanka albarkar Allah. Alqur’ani zancen Allah ne. Wallahi duk kuwa wanda ya kulla alaka da zancen Allah, ba zai taba tozarta ba, ba zai taba wulakanta ba duniya da lahira.

Kuma ku sani, Allah da kansa ya kira ma’abota Alqur’ani cewa sune iyalin sa, sune ahalin sa a cikin bayin sa.

Ya Allah, ka sanya ni, da ku, da sauran dukkanin ya uwana Musulmai cikin ma’abuta Alqur’ani, amin.

Wassalamu Alaikum,

Dan uwan ku: Imam Murtadha Muhammad Gusau, daga Okene, jahar Kogi, Nigeria. +2348038289761.

Share.

game da Author