Hukumar Tsaron Sojojin Sama ta Najeriya ta jibge zaratan sojojin ta 150, wadanda ta yi wa sansani na dindindin a Nguroje, Karamar Hukumar Sardauna, cikin Jihar Taraba.
Wadannan sansani na sojojin Kai Daukin Gaggawa, QRW, an kuma kafa su a Doma, cikin jihar Nassarawa da Agatu, cikin jihar Benuwai.
Babban Hafsan Sojojin Saman Najeriya, Sadique Abubakar, wanda ya yi wa rundunar jawabi a Jalingo kafin su karasa, ya hore su da su zama kwararru sosai wajen gudanar da aikin su.
Daraktan Gudanarwar Sojojin Sama, Napolleon Bali ne ya wakilci Abubakar, inda ya hore su da su ‘‘ tabbatar da cewa sun tsaya sun gudanar da ayyukan su a bisa ka’idojin Hukumar Tsaro ta Sojojin Sama da kuma dokokin da aka shimfida wa sojoji yayin da suka tsinci kan su cikin fama da artabu.’’
Yayin da ya ce su yi murna ganin sun samu wannan dama a matsayin su na kashin farko da aka dauka domin gudanar da wannan aiki, a daya gefen kuma ya hore su da su kulla kyakkyawar mu’amala da al’ummar yankin da aka girke su.
Ya ce bukatar a tabbatar da tsaro yadda za a samu ingantaccen tattalin arziki da kwanciyar hankali ce ta sa aka kafa sojojin a Nguroje, jihar Taraba.
A karshe Abubakar ya yi kira da su hada kai da sauran bangarorin tsaro domin a samu kyakkyawar nasarar da ake bukata.