Buratai ya tsima sojoji, maharan dajin Birnin Gwari, “kashin ku ya bushe”

0

Babban Hafsan Sojojin Najeriya, Tukur Buratai, ya bude sansanin sojoji a Birnin Gwari, cikin jihar Kaduna.

Ya bude sansanin ne a jiya Litinin, kuma aka sa masa suna Idon Raini.

An girke sojojin a kauyen Kamfanin Doka.

Da ya ke wa sojojin jawabi, Buratai ya umarci sojojin da su zakulo duk inda makasa jama’a suke a cikin dazukan a cikin kwanaki 21.

Ya kara horon sojojin da kada su sake su saurara wa kowane takadarin dan ta’addar da ya buwayi jama’a a yankin.

Buratai ya ci gaba da cewa labarin da kawai ya ke son ji shi ne a ce sojojin sun rattataki mahara da ke cikin dajin sun gama da su karkaf babu sauran wani takadari.

Ya kuma kara da cewa kada su yi wasarere har su kasance su yi sake ana kawo musu hari suna kare kan su.

Ya ce su kasance a koda yaushe su ne ke kai farmaki, ba wai su ake kaiwa ba.

Janar Buratai ya ce su sani fa cewa yaki aka kai su a yi, ba wasa ba. Don haka, ga fili nan, ga mai doki.

Buratai, ya yi wa sojojin jan-idon cewa yaki ne aka tsokane su, kuma ga su nan an girke, babu abin da ya rage musu, sai fatattakar tsagerun da ke cikin dazukan Birnin Gwari kawai.

“Tilas ku kawo karshen kashe-kashen da ake yi a cikin dajin nan, kuma tilas ku kawo karshen lalata dukiyyoyin da ake yi a cikin dajin nan na jihar Kaduna da sauran yankunan cikin kasar nan.

Buratai ya tsima sojojin da cewa, “maharan nan fa ba daga sama su ke saukowa su kai wa jama’a hari sannan su koma ba, su na nan cikin dazukan nan a boye.

“Don haka ban ga dalilin da zai sa ba za ku iya kutsawa cikin surkukin daji ku fatattako su ku gama da su ba.

Share.

game da Author