Kwanaki 10 bayan Daraktocin Bankin Duniya sun koma daga ziyarar gani da ido da suka kawo Najeriya, bankin ya bayyana cewa zai zuba dala bilyan 8.8, kwatankwacin naira tiriliyan 2.69 domin inganta wasu ayyukan ci gaba a cikin kakar shekarar 2019.
Wannan babban jari da Bankin Duniya zai zuba, za a yi ayyuka ne a karkashin hadin guiwa da cibiyoyin hada-hadar kudade, kamar IDA Bankin Kasa da Kasa na Sake Fardado da Al’umma da Cigaba, wato IBRD.
An sanar wa PREMIUM TIMES wannan batu ne a cikin wata takarda da Bankin Duniya ya aiko wa jaridar, kwanaki kadan bayan komawar daraktocin bankin daga ziyarar da suka kawo nan Najeriya.
A lokacin da suka kawo ziyarar, sun gamshu cewa tattalin arzikin Najeriya ya kara bunkasa sosai da sosai, kamar yadda tawagar daraktocin a karkashin jagorancin Patrizio Pagano suka tabbatar.
Pagano, wanda shi ne Darakta mai kula al’amurran kasashen Italy, Albania, Greece, Malta, Portugal, San Marino da Timor-Leste, ya ce sun zo Najeiya ne domin su fahimci alkiblar da tattalin arzikin kasar ya fi karkata, musamman a bangaren makamashi.
Baya ga tattaunawar da suka yi da Mataimakin Shugaban Kasa, Yemi Osinbajo da Ministar Harkokin Kudade, Kemi Adeosun, tawagar ta kuma ziyarci gwamnonin Adamawa, Bauchi, Borno, Gombe, Edo, Lagos, Taraba da Yobe.
Sun kuma dauki lokaci inda suka yi nazarin kalubalen matsalar tsaro a yankin Arewa-maso-Gabas da kuma Arewa ta Tsakiya, yankunan da Boko Haram suka fi yi wa illa da kuma fadace-fadacen makiyaya da manoma.
Bayan nazarin da suka gudanar, sun kuma kawo shawarwarin yadda za a inganta tattalin arzikin yankunan biyu.
Har ila yau kuma tawagar ta gana da wadanda suka ci moriyar tallafin harkokin aikin noma na Bankin Duniya da wadanda suka ci moriyar na harkokin ilmi, kiwon lafiya, tallafa wa matasa, raya yankunan karkara, zaizayar kasa da sauran su.
Discussion about this post