Har yanzu mutanen Mubi, jihar Adamawa na fama da yaduwar cutar Kwalara

0

Jami’in yada labarai na ma’aikatar kiwon lafiya na jihar Adamawa Abubakar Muhammed ya bayyana cewa tsakanin kananan hukumomin Mubi ta kudu da Mubi ta Arewa jihar ana samun karuwar mutanen da ke kamu da cutar Kwalara.

Muhammed yace a yanzu haka mutane 434 sun kamu da cutar sannan ta yi ajalin mutane 13 a jihar.

” A Mubi ta Kudu mutane 223 sun kamu da cutar sannan mutane 6 sun rasa rayukan su, a Mubi ta Arewa kuma mutane 211 ne suka kamu da cutar sannan 7 sun rasa rayukan su.”

A karshe jami’in babbar asibitin Mubi Ezra Sakawa ya ce mafi yawan mutanen da suka kamu da cutar an sallame su.

Share.

game da Author