Wani matashi dan kasar Mali ya zama dan kasar Faransa bayan ceto dan yaro mai shekaru hudu da daga kololuwar gidan sama yana ririto zai fado.
Shi dai wannan matashi mai suna Mamoudou Gassama, ya fito daga inda ya ke zama ne a matsayin sa na bakon haure a kasar Faransa, domin ya kalli kwallon kafa a unguwar, sai ko ya hango anyi cincirundo ana kallon ikon Allah, dan yaro a can sama yana ririto zai fado, a gefe kuma ga iyayen sa can suna kokarin riko hannun sa.
Nan da nan Mamoudou ya kama ginin yadda kasan gizo-gizo yabi bango yana kamawa har ya kai ga wannan dan yaro ya ko rikoshi cak. Ya haura ya mika wa iyayen sa.
A can kasa kuma wasu na daukar wannan jarumta da Mamoudou yayi, bayan haka suka sassaka a shafunan yanar gizo ana ta yaba masa.
Yabon bai tsaya nan ba, shi kan sa shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron, ya gayyace shi ofishin sa ya yi masa godiya sannan ya amince a maidashi dan kasa. Bayan haka an dauke shi aiki nan take a ma’aikatar kashe gobara na kasar.
Masu sharhi da yawa sun ce abin da yayi a shirin fim ne kawai suka taba gani.

Gwamnati ta maka mahaifin wannan dan yaro a kotu, cewa yayi sakaci wajen barin dan sa ya kai har wannan wuri da Allah yasa yana da sauran rayuwa a duniya. An ce mahaifiyar sa ta tafi aiki ne shi kuma mai gidan ya dan fita maza-maza ya siyo wani abu a shago.