Sai ka yi Ilimi kan kiwon lafiya zaka rike mukami a kungiyar mu

0

Kungiyar ma’aikatan lafiya reshen jihar Legas sun bayyana cewa daga yanzu duk wanda zai zama sakataren kungiyar dole sai ya na da ilimi na kiwon lafiya.

Kungiyar ta fadi haka ne a taron da ta yi a jihar Legas inda ta bayyana cewa dora wanda bai karanci aikin asibiti ba a wannan kujera ya saba wa dokar kafa kungiyar.

Kungiyar ta kuma kara da cewa ba za ta amince da yunkurin da gwamnatin jihar ba na saka masana magunguna da masu gwajin jini da sauransu cikin wannan kungiya ta su ba.

Share.

game da Author