Duk da irin yadda Gwamnatin Muhammadu Buhari ta zama magorin da ke wasa kan sa da kan sa, ta na bugun kirjin cewa ta gudanar da gagarimin abin a zo a gani, wata kuri’ar jin ra’ayin jama’a da mutane 4,000 suka kada ra’ayin su ta nuna cewa Buhari ya kasa tsallake siradin sa.
Inda ra’ayin ya fi karkata shi ne, duk da tsallen da shugaban ya tuma, amma ya kasa tsallake siradin matsalar tsaro, tattalin arziki da kuma ta yaki da cin hanci da rashawa.
Amma kuma a ranar Juma’ar da ta gabata, Fadar Shugaban Kasa ta fito da wani kundi, inda ta yaba wa kanta abin da ta kira gagarimin ayyukan da ta yi a fannin tattalin arziki, ababen more rayuwa, zuba jari ga al’umma da sauran su.
Sai dai kuma kuri’un jin ra’ayin sun nuna cewa Buhari ya kasa cika wa ‘yan Najeriya alkawurran da ya dauka kan inganta tattalin arzikin kasa, tsaro da kuma cin hanci da rashawa.
‘Yan Najeriya sun yi amfani da kuri’u suka kori PDP daga mulki, bayan ta shafe shekaru 16, amma ta kasa magance babbar matsalar da ta fi addabar kasar nan, wato mamayar Boko Haram.
An kori PDP ne a bisa amanna da alkawarin da Buhari da kuma jam’iyyar sa ta APC suka rika yi cewa, su ne ke da maganin warkar da duk wani ciwon da ke damun Najeriya idan sun hau mulki, za su magance shi, sha-yanzu-magani yanzu.
Bayan shekaru uku kan mulki, rahoto ya nuna ‘yan Najeriya na cewa Buhari ya kasa daura cikkakkar alwala, amma da farko an yi tsammanin ya ma iya salloli biyar wajibai da ke kan sa.
Kungiyar CCD, mai bin hadi da sa-ido kan dimokradiyya ce ta dora Buhari kan siradi, inda ta rika bibiyar alkawurran da ya dauka domin a tantance, ganin cewa a yau cika shekara uku kan mulki, sauran sa shekara daya tal a wannan zango.
CCD ta ce an ji ra’ayoyin jama’a har 4,000 daga kowace jiha 36 da Abuja.
Dukkan ra’ayoyin ta hanyar buga wayar tarho aka tattara su.
Kashi 40 sun yarda cewa Buhari ya yi kokari, yayin da kashi 44 suka ce ya yi bazata, bai kai yadda suka yi tunanin zai yi ba kafin a zabe shi. Sauran kashi 16 kuma ba suce ya yi kokari ko bai yi ba.
Hakan kuwa ya nuna yadda farin jinin shugaban ya ke raguwa idan aka kwanta da jin ra’ayin jama’a da aka yi na 2017, bayan da Buhari ya shekara biyu a kan mulki.
A shekarar 2017 an samu kashi 57 wadanda suka yaba masa. Amma yanzu a 2018 kashi 40 kawai aka samu. Wato farin jinin sa ya ragu da kashi 17 daga cikin wadanda suka yabe shi a 2017 kenan.
Wannan kuwa na nuni da cewa wadanda ba su ganin kokarin na sa su ne ke karuwa, ba masu ganin kokarin sa ba.
Kashi 67 bisa 100, sun ce tattalin arzikin Najeriya tangal-tangal ya ke yi. yayin da a 2017 kashi 39 ne kadai suka ce bai tabuka komai a fannin tattalin arziki ba.
Su na ganin duk wani dogon Turancin da wasu masana da ke jikin gwamnati ke yi, da wata kididdigar kan takarda, duk shirim ba ci ba ce, tunda har yau jama’a, musamman masu karamin karfi na cin kwakwa, babu sassauci.
Kashi 57 bisa 100 sun ki yaba wa Buhari a kan yaki da cin hanci da rashawa wanda gwamnatin ke yaba wa kanta cewa ta samu gagarimar nasara a fannin.
A fannin tsaro kuwa kashi 55 sun nuna bacin ran su ga gwamnatin Buhari da shi Buharin kan sa, kashi 21 ne suka jinjina masa. Yayin da kashi 24 kuma suka ce kadaran-kadahan.
Haka bai samu yabo a harkar lantarki, lafiya, ilmi, sufuri. Amma an nuna yac dan tabuka a fannin harkar noma.