An kashe ‘yan sanda uku, an yi garkuwa da wani dan kasar Siriya a Sokoto

0

Jami’ar hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Sokoto Cordelia Nwawe ta bayyana cewa wasu mahara sun kashe ‘yan sanda uku uma sun yi garkuwa da wani dan kasar Siriya mai suna Abdul Nasir a kauyen karamar hukumar Bodinga.

Cordelia ta ce wannan abu ya faru ne da karfe 7 na safe a harabar kamfanin gine-gine na ‘Triacta Construction Company’ dake kauyen Lambar Mazaru a karamar hukumar Bodinga.

Ta ce rundunar ta fara yin bincike akai domin ceto wanda aka dauke da kuma kama wadannan masu garkuwa da mutane.

Wasu cikin masu gadin kamfanin da abin ya faru a idanuwar su sun bayyana wa manema labarai cewa maharan sun zo ne a mota sanye da bakaken gilasai sannan suka harbe wadannan ‘yan sanda uku Kafin suyi garkuwa da Abul Nasir wanda shine manajan Kamfanin.

Share.

game da Author