A ranar Talata ne gwamnatin jihar Yobe ta amince da yi wa ma’aikatan jinya dake yajin aiki a jihar karin albashi.
Kakakin gwamnan jihar Abdullahi Bego ne ya sanar wa PREMIUM TIMES haka, in da ya ce gwamnati ta yi haka ne domin ma’aikatan su samu su dawo aiki asibitocin kasar nan.
” Yanzu dai ma’aikatan jinya dake jihar Yobe za su fara karban albashi daidai da na ma’aikatan gwamnatin tarayya.