Kungiyar Koli da ke kula da harkokin addinin Musulunci NSCIA ne ta sanar da ganin watan, in da tace gobe ne 1 ga watan Ramadan.
Bayan haka sarkin Musulmai Abubakar Sa’ad ya sanar da ganin watan a jihohin Sokoto, Niger, Yobe, Port Harcourt, Borno, Gombe, Jigawa da wasu wurare da dama.
Shugaba Muhammadu Buhari ya yi wa musulmai fatan Alkhairi da yin Ibada karbabbiya.