APC a 2019: Hasashe 14

0

1.A daina kallon taron mutanen da ke zuwa kallon shugaban kasa idan ya kai ziyara garuruwa. Akasarin su ba rajista gare su ba. Wasu kuma ‘yan siyasar yankin su suka dauki shatar motoci aka kai su wurin taro.

2. Irin yadda Buhariyya ta zama guguwa a wancan zaben, a wannan karon ba za a yi hakan ba.

3. Mabiya Shi’a masu dimbin yawa sai yankar rajista su ke yi domin ramuwar-gayya kan APC da jihar Kaduna da kuma kan zaben shugaban kasa.

4. Yarabawa kuma baki-biyu gare su. Kuma ba lallai ba ne APC ta sake samun Kuri’un da ta samu a yankinnKudu-maso-yamma.

5. A jihar Katsina, Kaduna, Zamfara, Benuwai, Taraba, Kano, Kogi, Nasarawa da wasu jihohi, da wahala ta samu yawan kuri’un da ta samu a 2015, idan zaben 2019 ya zo.

6. Wanda ke tababar hasashe na 5, ya binciki adadin wadanda suka yanki rajista a ofishin INEC ya sha mamaki.

6. A Arewa, Kano ce aka fi yanka da yawa, kuma binciken ra’ayin da wasu suka yi, ya nuna ‘Bani Kwankwasiyya’ ne suka fi yanka, domin su yi ramuwar-gayyar tozarta ubangidan su da aka yi.

7. Irin su Kwankwaso hakuri ya kamata ku rika ba su, ba a tsaya a na adawa da su ba. Irin su El- Rufai ja-musu kunne ko taka musu burki ya kamata a yi, dominn matsalar su biyun matsalar APC ce.

8. Kwankwaso ko bai tsaya takara ba zai yi wa APC illa a ‘anti-party.’

12. Magoya bayan APC a yanzu ba su da kuzari ko jan-idon da za su zare wa magoya bayan PDP a ranar zaben, har su ji tsoron fitowa su zabi wanda su ke so, kamar yadda aka yi zaben 2015.

13. irin yadda aka rika makala wa magoya bayan PDP ‘kaulasan’ a 2015, wannan ba zai yi tasiri ba a zaben 2019, har wasu su ji tsoron fita su jefa kuri’a, gudun kada a tozarta su, kamar yadda aka rika yi wa wasu ‘yan PDP a zaben 2015.

14. Ko ma dai me kenan, APCn yau ba ta da karsashi da guguwa irin ta jiyar 2015.

Share.

game da Author