Muddun gwamnati ta biya bukatan ma’aikatan jinya, muma za mu fara yajin aiki – Kungiyar likitoci

0

Kungiyar likitocin Najeriya (NMA) ta gargadi gwamnati cewa Kada ta kuskura ta amsa koke-koken Kungiyar ma’aikatan jinya wato JOHESU cewa tayi watsi da su kawai domin Idan ta biya musu bukatun su lallai suma za su fara yajin aiki.

Idan ba a manta ba kungiyar JOHESU ta shiga yajin aiki ne tun 17 ga watan Afrilu.

Wannan yajin aiki ya Kawo cikas ga ayyukan asibitocin kasar nan.

” Idan har gwamnati ta biya wannan bukatu nasu to lalle fannin kiwon lafiya na kasar nan za ta daina aiki kwata kwata.”

Shugaban kungiyar Francis Faduyile ya rubuta wa gwamnatin tarayya wasikar tunin wasu alkawura da gwamnati ta dauka wa Kungiyar.

” Muna gaba da JOHESU sannan muddun Gwamnati ta biya musu bukatunsu za mu shiga yajin aikin gama gari a kasar nan. Sauki sa shine kada su saurari ma’aikatan kiwon lafiya.

Share.

game da Author