Tashin farko, tunanin da na yi bayan kafa jam’iyyar gamin-gambiza mai suna APC, za su koyi darasi daga tarihin kafa gambizar siyasar can baya, su tashi haikan wajen kafa jam’iyya, maimakon kafa manyan cikin ta kawai. Na yi zaton bayan yi wa jam’iyyar rajista za ta rika yawo kwararo-kwararo, kauye-kauye su na yi wa talakawa rajistar shiga jam’iyyar kamar shigar-farin-dango.
Maimakon haka, kacokan abin da APC ta raja’a yi a lokacin, shi ne yadda jam’iyyar za ta ci zabe da karfin yawan kuri’u kawai. Babu ruwan ta da kai ko ma daga ina aka fito, duk akidar ka ko ra’ayin ka, in dai za ka jefa mata kuri’a ta ci zabe, to gaba ta kai jam’iyyar, shikenan.
Sai ya zamana jam’iyyar ba ta da yawan mambobi, amma ta na da dimbin magoya baya. Duk da haka, wannan bai kara wa jam’iyyar tasiri ba, har sai da PDP, jam’iyyar da ake so a kawar ta samu matsala, daga nan ne kuma duk wandada APC ke zagi su na cewa su suka kashe Najeriya, sai suka rika ficewa su na komawa jam’iyyar APC da ke neman kawar da su daga mulki, su na yin kaka-gida a can.
Dalili kenan Buhari ya samu nasarar kafa mulki tare da dimbin wadanda a baya su ne suka zame masa shingen hana shi kaiwa ga samun nasara. Su din ne kuma ya rika cewa sunn tafka masa magudi a zabukan baya da ya tsaya takara.
A lokacin guda kuma Buhari ya hau mulki bayan ya rabu da yawancin wadanda suka rika fafutika ba dare ba rana, wajen ganin ya samu nasarar hawa mulki a zabukan da ya fito takara can baya. A takaice kenan, makiyan sa sun koma masoyan sa, masoyan sa kuma sun koma makiyan sa.
Da yawa daga cikin gaggan ‘yan PDP da mulki ya subuce daga hannun su can baya, su ma sun rika komawa APC su na samun tikitin komawa kan mulki, walau a gwamna ko kuma mukaman sanata da na majalisar tarayya.
Da yake APC dama neman mulki ke gaban ta, ba gina jam’iyya ba, tun ba ta cika shekara daya kan mulki ba ta shiga rigingimu. Duk wanda ya yi magana sai su ce ai dama siyasa ta gaji haka, maimakon su magance matsalar ko su raja’a wajen gina jam’iyya. Har sai da ta kai jam’iyyar a yanzu ta rikice, ta kacame, ta na ma neman balbalcewa.
Shi kan sa Shugaba Muhammadu Buhari, bai maida hankali wajen gina jam’iyya ba. Tun da aka kafa APC bai je wasu jihohi ba har sai gab da magriba sati daya kafin kafin zabe, kuma iyakar sa filin taro kawai. Har ila yau tun da ya hau mulki, shekara uku kenan cur, amma babu wata kwakkwarar rashin jituwar manyan ‘yan jam’iyya da ya sasanta, sai ma wadanda ke ta kara tafarfasa.
Irin yadda ake samun barakar da ke keta jam’iyya na nuna cewa babu mai jin maganar Buhari ko da ya tsawatar, ko kuma ba shi ma da bakin tsawarwa. Duk shugaban da ke neman kuri’a a Najeriya ba zai iya barci mai nauyi ba idan daurin zanin jam’iyyar ya sakwarkwace a jihar Kano da Kaduna. Domin kuwa a ranar zabe zigidir za a yi masa.
An manta da halin da kwamitin Bola Tinubu na sasanta ‘ya’yan jam’iyya ya ke ciki. Da alama shi kan sa Tinubu ya jefa kwamitin a cikin kwandon shara, tunda ya ga bukatar sa ta cire shugaban APC Odigie Oyegun a nada Adams Oshimhole za ta tabbata.
An yi mamakin da har yau Shugaba Buhari ko manyan APC ba su ce komai dangane da abin da aka kira kalaman kiyayya da tsinuwar da gwamnan jihar Kaduna Nasiru El-rufai ya yi wa sanatocin jihar uku ba, abin da ake kallon cewa zai iya haifar wa APC matsala a jihar Kaduna.
Dalilai a kwanan nan sun kara tabbatar da cewa APC gambiza ce, ba jam’iyya ba ce sun kara fitowa fili kwanan nan a zabukan shugabannin shiyyoyin mazabu na fadin kasar nan da jam’iyyar ta gudanar a ranar Asabar da ta gabata. An yi kisa, an sace akwatu, an yi magudi, an yi dauki-dora, an baddala sunaye, an sauya sunayen wadanda suka yanki fam da na wadanda ba su fito neman mukamai ba. Ba a yi zabe ba amma an fito an yi rantsuwa da Allah an ce an yi zabe. An yi dake-dake. An yi sare-sare, an kuma yi kone-kone duk a fadin kasar nan kan zaben shugabannin jam’iyya na mazabu kawai.
Jiya Juma’a a Fatakwal magoya bayan Sanata Magnus Abeh da na Ministan Sufuri Rotimi Ameichi sun dira cikin Babbar Kotun Jihar har sun kashe mutum biyu. Duk wannan shirme da hauka da harigido da harkalla, su ne fa APC ta shafa wa talakawa mai ga baki suka rika yin tir da PDP saboda an yi musu alkawarin tsayar da gaskiya da adalci a cikin jam’iyya.
UNGULU DA KAN ZABO
Duk yadda mai karatu zai yi kokarin tantance APC daga PDP, hakan ba zai yiwu ba, sai dai kame-kame da kawo tawili maras gamsasshen dalili. Gwamnonin APC 24, amma 17 duk gyauron PDP ne. Audu Ogbe da Barnabas Gemade kuwa har shugabancin PDP a Najeriya sun yi. Akwai tsoffin gwamnoni wadanda a yanzu sanatoci ne a karkashin APC irin su Rabi’u Kwankwaso, Abdullahi Adamu, Aliyu Wamakko, Danjuma Goje, Adamu Aleiro, Shugaban Majalisar Dattawa Bukola Saraki da sauran kusan dozin biyu wadanda asalin su PDP ne.
Kakakin Majalisar Tarayya Yakubu Dogara dan PDP ne. Barnabar Gemade da Minista Audu Ogbe kuwa har shugabancin jam’iyyar PDP sun taba yi dungurugum, amma yanzu su ne gwamnatin APC. Akwai kuma daidaikun jiga-jigai da wasu Sanatoci irin su Ali Ndume da a da can ‘yan PDP ne, amma yanzu duk su na APC.
TARON TSINTSIYA BA SHARA
Irin yadda ake tafiyar da jam’iyyar da irin yadda ta ke cikin rigingimu ba shi da wani bambanci da PDP. Kamar yadda wasu ke cewa, Shugaba Muhammadu Buhari ne kawai da Mataimakin sa Yemi Osinbajo kadai bambanci tsakanin APC da PDP.
Cikin makon da ya gabata ne rukunin hasalallun da su ka balle daga PDP suka kafa nPDP wadda ta shiga gambizar APC suka rubuta takardar korafin cewa gwamnatin Muhammadu Buhari ta mayar da su saniyar-ware. Kowa dai ya san nPDP, wadanda ba don su ba, da APC ba ta kafa gwamnati a Najeriya ba.
Daga cikin gangamin zugar nPDP babu wanda aka ba mukamin minista sai Rotimi Ameichi shi kadai. Haka kuma babu su a manyan mukamai na tarayya a matsayin shugabannin hukumomin gwamnati da sauran su. Wadanda su ka yi wa kan su ‘kiyamul laili’ ne kadai suka tsira da mukaman sanatocin da suka nema, su din ma kamar irin su Kwankwaso, nema ake yi a barar da su.
Hangen wannan biyu-babu ne ya sa Bukola Saraki da sauran sanatocin nPDP suka fahimci za su tashi a turar ko-oho, ta sa suka tashi tsaye suka kwace mukamin Shugaban Majalisar Dattawa aka nada Saraki. Domin ita jam’iyyar APC Sanata Ahmed Lawan ta so a ba mukamin.
Sun fito sun bayar da wa’adin kwanaki bakwai, ko dai a gyara ko kuma kowa ya kama gaban sa. Ashe APC din da mu ke tinkaho da ita, taron tsintsiya ce amma ba shara? Shin mene ne makomar APC idan nPDP suka balle a cikin ta, ko kuma suka haifar mata da matsala a wannan mawuyacin halin da jam’iyyar ke ciki?
MAFARKIN APC A 2019
Su dai talakawa a yanzu sun kasu kashi biyu: Kashi na farko akwai ‘yan Buhariyya na gidi, wadanda duk kuskuren gwamnatin APC, ko da ya fi irin wanda PDP ta yi muni, to ba su kallon abin a matsayin kuskure. Sannan kuma har yau su na kwana da tashi da mafarkin cewa irin yadda aka yi wa Buhari guguwa a 2015, haka za a yi masa a 2019.
Irie-iren wadannan ba su kallon akwai matsala a Kano, Kaduna, Oyo da jihohi da yawa inda ke nuna alamomin za a yi wa APC ‘anri-party’ can a tsakanin magoya bayan jam’iyyar.
Har ila yau kuma su gani suke yi kuri’un da Buhari ya samu a jihohin Filato, Nasarawa, Taraba, Adamawa da Benuwai a 2015, duk zai sake samun su a 2019.
Yawancin su sun manta da cewa Buhari ya tsaya takara sau uku, bai yi nasara ba sai da guguwa ta tarwatsa garken PDP wasun su suka shiga cikin APC tukunna.
Rabo na biyu na gungun talakawa na ganin cewa su fa sun sha rana, sun sha wahala, amma har yau ba su ga canjin da ake magana ba. Yawancin alkawurran da aka yi musu a kan takarda ko a kan duro, duk ba su tabbata ba sai ma kara ta’azzara da matsalar ta yi.
An yi musu alkawarin shan man fetur da arha, a maimanon haka, an kusa ma nunka masa kudi. Har yau dala ta ki saukowa daga tsadar da ta yi, kuma farashin kaya ya ki sauka.
BA A RABU DA BUKAR BA….
An samu saukin Boko Haram a Arewa, in banda Barno da Yobe, amma kuma an wayi gari da sabon salon kashe-kashe a Benuwai da Taraba da Kaduna da Zamfara. Abin kullum sai kara muni ya ke yi. An wayi gari a Arewa sace mutum a yi garkuwa da shi ya fi satar yankan aljihu sauki.
Irin wadannan dalilai sun sare guyawun dama wadanda suka bi bayan APC a 2015, amma yanzu da yawan su ba za su ko fito su yi zabe a 2019 ba.
Irin yadda hukumar zabe ke shelar a fito a karbi rajista, INEC ta ce akwai kusan rajista ta mutane milyan bakwai da suka yi can baya, amma sun ki zuwa su karba. Hakan na nuni da cewa da yawa ba su marhabin kuma ba su rawar jikin tilas sai sun jefa kuri’a a 2019. Don me? Saboda wasu gani su ke yi yau din dai kamar jiya ta ke.
Yanzu da ake cikin fama da yajin aikin likitoci da malaman asibitoci, da dama na ci gaba da yi wa APC korafin tuna musu alkawarin da ake cewa Buhari ya yi na gyara asibitoci a daina fita waje neman magani. Sun fara yi wa APC gorin cewa an bar su babu masu duba lafiyar su, shi kuma shugaban kasa ya kasa magance matsalar, amma ya fice waje ganin na sa likitan a saukake.
LEGAS: ’Yarlelen Gwamnatin Buhari
Su na kuma kukan cewa duk da wahalar da suka sha wajen tula wa APC kuri’u, shekara uku kenan ana mulki amma ba a yi wa Arewa wasu ayyuka na zo a gani ba, an bar su da zafin kishin jam’iyya ko Buhariyya. Wadannan ba’arin talakawa su na jin haushin yadda gwamnatin Buhari ke ta kashe kudade ta na gudanar da ayyuka a jihar Legas.
Sannan kuma akwai korafin cewa a duk lokacin da Buhari ba ya kasar, sai mataimakin sa Osinbajo ya sa hannun amincewa da kara damfara wasu makudan kudade a wasu ayyuka da ake yi a Legas ko kuma sa hannun amincewa a kirkiro wasu da za a kashe makudan kudaden da ba a kashe su kakaf a Arewa ba.
Dama kuma su APC bangaren nPDP, sun koka da yadda ba a ba su mukamai a ministoci ba. Hakan kamar wani nuni ne su ke yi da yadda Buhari ya dauki mukamin manyan ministoci uku, na ayyuka, makasmashi da kuma na gidaje, duk ya damka su ga mutum daya, Fashola, tsohon gwamnan Legas, wanda ake ganin kamar ya zama ministan raya jihar Lagas din ba ministan Najeriya ba.