YAJIN AIKIN JOHESU: Ba mu daidaita da gwamnati ba – Ogbonna

0

Mataimakin shugaban kungiyar ma’aikatan jinya JOHESU Ogbonna Chimela ya bayyana cewa har yanzu kungiyar ba ta daidaita da gwamnati ba game da yajin aikin da ma’aikatan jinya ke yi a kasar nan.

Ogbonna ya bayyan wa PREMIUM TIMES cewa gwamnati ta yi musu tayi amma kungiyar na yin nazari kan da wannan tayi.

” Mun zauna da gwamnati ranar Laraba inda ta yi mana tayi amma za mu yi nazari a kai domin ganin ko wannan tayi da gwamanti ta yi mana zai karbu a gare mu ko a’a.”

A yanzu haka yajin aikin da JOHESU ta fara ya shiga mako na hudu kenan sannan ma’aikatan jinya dake aiki a asibitocin jihohi da kananan hukumomi suma sun bi sahu su.

” Muna nan kan bakar mu musamman yanzu da muka sami goyan bayan ma’aikatan jihohi da na kananan hukumomi.”

Ya ce za su ci gaba da tattaunawa da gwamnati kan bukatunsu a yau Alhamis da karfe takwas na dare.

Share.

game da Author