YAJIN AIKIN JOHESU: Zamu ci gaba da kula da marasa lafiya a asibitocin gwamnati – Likitoci

0

A yau Alhamis ne kungiyar likitoci na kasa (NMA) reshen jihar Ondo ta yi kira ga gwamnati da ta samar wa likitoci kariya a asibitocin jihar musamman a wannan lokaci da kungiyar ma’aikatan jinya (JOHESU) ke yajin aiki.

Shugaban kungiyar Arohunmolase R.B ya sanar da haka wa manema labarai inda ya kara da cewa kungiyar su sun lashi takobin ci gaba da kula da mara sa lafiya duk da cewa ma’aikatan jinya.

Idan ba a manta ba kungiyar NMA ta yi kira ga gwamnati da ta yi watsi da bukatar JOHESU na neman karin albashi.

‘‘Muna tabbatar wa gwamnati cewa za mu ci gaba da kula da marasa lafiya a duk asibitocin kasar nan na tsawon awowi 24.”

A karshe Arohunmolase ya jinjina wa likitocin kasar nan na ci gaba da kula da marasa lafiya da su ke yi a asibitocin kasar nan.

Share.

game da Author