Daga yanzu Hukumar Alhazai za ta tantance ‘yan jaridan da za su dauko rahotanni a aikin Hajji

0

Shugaban Hukumar Alhazai ta kasa, Abdullahi Mukhtar ya bayyana cewa hukumar zata fara tantance ‘yan jaridar dake dauko rahotanni daga kasar saudiyya lokacin aikin Hajji.

Mukhtar ya fadi haka ne a zauren taron kaddamar da sabuwar shafi na yanar gizo mai suna ‘Kungiyar ‘yan jarida masu aiko da rahotannin aikin Hajji mai zaman kanta’ da aka yi a Abuja ranar Alhamis.

Shugaban hukumar Alhazan ya koka kan yadda wasu ‘yan jarida ke rubuto labaran karerayi a lokacin aikin Hajji da hakan kan wuce gona da iri har ya shafi diflomasiyya na tsakanin kasa da kasa musamman wanda ya shafi Najeriya da Kasar Sa’udiyya.

” Idan har za ace a wasan kwallo ma sai an tantance ‘yan jaridar da zasu watso labarai, ya kamata ace a aiki mai muhimmanci kamar aikin Hajji ma ana tantance wadanda za su yada abubuwan dake faruwa a can.

Ya ce dole a horas da ‘yan jarida su san irin abubuwan da zasu na dauko wa suna yadawa domin gujewa wuce gona da iri.

Ya yabawa wannan shafi da wannan kungiya ‘IHR’ ta kirkiro cewa kada su maida ita sai su kadai, su nemi shawarwari daga mutane sannan su bar kofofin su ga kowa da kowa domin abu ne na ci gaban addini.

Mataimakin shugaban masu rijaye na majalisar dattawa, Bala Ibn Na’Allah ya yabawa wa wannan kungiya sannan ya hore su da su maida hankali wajen sanar wa mutane abubuwan da ake fadi da ba daidai ba a wasu kafafen yada labaran game da aikin Hajji.

” Wannan wata dama ce da zaku gyara kurakuren da ake yadawa game da aikin Hajji ta wannan shafi na ku.”

A nashi tsokacin Kodinatan wannan Kungiya, Ibrahim Mohammed, cewa yayi daya daga cikin dalilan da ya sa suka kirkiro wannan shafi shine don su samar da wata kafa da za a samun sahihan labarai game da aikin hajji da umra da wasu ababen da zai amfani mahajjaci, da sauran musulmai game da aikin Hajji, Umrah da sauran su.

Ya ce bawai bukin bude shafin bane kawai ya tara su a wannana wuri, sun shirya ba da kyaututtuka na karramawa ga wadanda suka bada gudunmuwar su a kan harkokin aikin hajji a kasar nan.

Wadanda aka karrama sun hada da Gwamnan jihar Barno, Kashim Shettima, tsohon gwamnan jihar Katsina Sa’idu Barda, tsohon gwamnan jihar Kano Ahmed Daku, Ministan Abuja, Muhammed Bello da Hukumar jindadin Alhazai na jihar Legas da na Kaduna.

Sauran sun hada da Sanata Jibril Aminu, Honarabul Haruna Yerima, Gwamnan Jihar Kaduna Nasir El-Rufai, tsohon shugaban Hukumar EFCC, Nuhu Ribadu, Babban Bankin Najeriya (CBN) da Gidan Tabijin na Kasa (NTA).

Gwamnan jihar Barno ya tallafa wa kungiyar da naira Miliyan Biyu.

Ga adireshin shafin:www.hajjreporters.c.om

Share.

game da Author