Ko ka san cewa wanke hannu don tsafta na kare ka daga manyan cututtuka?

0

Wanke hannu hanya ce ta tsaftace jiki dake kare mutum da sauran mutanen dake kusa da shi kamuwa da cututtuka masu wahalan magani.

Bayanai sun nuna cewa likitoci da ma’aikatan jinya sun fi kamuwa da kuma yada cuta da hannun su saboda kin wanke hannu da suke yi a aikin su.

” Bincike ya nuna cewa kashi 15 na maza da kashi 5 na mata a Najeriya basa wanke hannuwan su bayan sun yi amfani da bayi.” Inji Hukumar NCDC

” Rashin wanke hannu da ruwa da sabulu ba da ruwa ba kawai na sa a kamu da cututtuka kamar su amai da gudawa, mura,da sauran su.” -Inji Hukumar NCDC

Domin guje wa irin wannan matsaloli hukumar hana yaduwar cututtuka na kasa (NCDC) ta bayyana cewa kamata ya yi a wayar wa mutane kai don sanin mahimmancin tsaftace muhalli da wanke hannaye da ruwa da sabulu.

Share.

game da Author