Wani Mai’unguwa da mutane biyu sun hadu da ajalin su, yayin da wasu mahara suka bindige su a yammacin Lahadi, a jihar Filato.
Shugaban Riko na Karamar Hukumar Barki Ladi, Dickson Chollom ne ya bayyana haka a yau Litinin, ya kara da cewa an kashe basaraken ne a cikin gidan sa, su kuma sauran biyu an bindige su ne a cikin shagon wani mai aski, a cikin garin Barikin Ladi.
“A yanzu da na ke magana, Gwom Rwei Gashis ya na can an kwantar da shi Babban Asibitin Barkin Ladi, mutu-kwakwai-rai-kwakwai, sakamakon harbin da aka yi masa.’’
Shugaban Karamar Hukumar ya ce sojojin kiyaye zaman lafiya na “Operation Safe Heaven ne suka kai masa rahoton harin da aka kai.
“An tabbatar min da cewa an kai wa gidan basaraken gargajiyar hari, har kuma an cinna wa gidan wuta.”
Har ila yau, ya ce daya daga cikin wadanda tsautsayin harin ya ritsa da su a cikin shagon mai aski, shi kuma an dauke shi daga asibitin Barkin Ladi zuwa Babban Asibitin Jos, ganin irin mummunan halin da ya ke ciki.
Wadanda aka harba a cikin shagon askin su ne Danladi Adamu da Rapheal Pwajok. An harbe su a daidai mahadar hanyar Barkin Ladi da Bakkos.
Sai dai kuma shugaban karamar hukumar ya tabbatar da cewa cikin kwanakin nan, an satar wa makiyaya shanu kimanin 400, amma jami’an tsaro da ‘yan bijilante da shi kan sa shugaban karamar hukumar sun yi kokari kwarai wajen hana barkewar mummunan rikici a sanadiyyar sace shanun.
Ya ce har yanzu su na ta fafutikar neman inda shanun su ke domin maida wa masu abin su.
Daga nan sai ya yi kira da a zauna lafiya da juna.
Discussion about this post