Bayanai sun nuna cewa shaye-shayen maganin tari da ke dauke da ‘Codein’ ya zamo ruwan dare a kasar nan musamman a yankin Arewa sannan matan aure da mata masu ciki ba a barsu a baya ba game da haka.
Sanadiyyar haka ne a makon da ya gabata gwamnati ta hana shigowa da sarrafa wannan maganin domin ceto rayukan mutanen kasar nan daga illolin dake tattare da shan wannan maganin.
1. Shan maganin ‘Codine’ na hana mutum iya yin tunani yadda ya kamata sannan yana yin illa ga Hanta, Koda da huhun mutum.
2. Hana shigowa da sarrafa maganin ba shine zai hana siyar da maganin ba domin irin babbar kasuwa da take da shi a Najeriya.
3. Bincike ya nuna cewa banda shigowa da maganin da ake yi kamfanonin sarrafa magunguna a kasar nan na sarrafa maganin.
4. A kan siyar da kwalban maganin akan Naira 1000 zuwa 1,200 amma hakan bai hana masu sha- siya ba
5. Ko ba tare da izinin likita ba ana iya samun maganin a shagunan siyar da magunguna a kasar nan.
6. Mafi yawan mawakan kasar nan na taimakawa wurin hassasa amfani da wannan maganin domin a ganin su maganin na taimaka musu wuri raira waka.
7. Maganin kan sa maye, jiri, gane gane wasu abubuwa idan an sha.
8. Bincike ya nuna cewa matasan arewa ne suka fi amfani da wannan magani.
9. Jami’an tsaro sun kama sama da miliyan uku na kwalaben maganin a jihohin Kano, Jigawa da Katsina.
10. Hukumar NAFDAC ta mota dankare da kwalaben maganin da ya kai 24,000 a jihar Katsina.