Rubabbun Kwan dake PDP sun koma wasu jam’iyyun, gangariya suka rage yanzu, Inji Makarfi

0

Tsohon gwamnan Jihar Kaduna kuma jigo a jam’iyyar PDP, Ahmed Makarfi, ya fadi a taron jam’iyyar na shiyyar Arewa Maso Yamma da akayi a garin Katsina cewa yanzu a PDP babu wani baragurbi a cikin ta, cewa duk lalatattun Kwan sun fice sun koma wasu jam’iyyun.

Tsohon gwamnan Kano, Ibrahim Shekaru, shima ya roki mutane ne da su tabbata sun yi rijistan katin zabe.

Sannan ya roki ya’yan jam’iyyar a Jihar da su ci gaba da zama tsintsiya madaurinta daya domin samun nasara a zabukkan dake tafe.

Shi ko Shugaban jam’iyyar na kasa Uche Secoundus yabawa mutanen Katsina yayi cewa har yanzu Jam’iyyar na da magoya baya masu dimbin yawa a Jihar.

” Babu abin da zan ce wa mutanen Jihar Katsina sai godiya don ko dandazon jama’a da na gani a nan nuni ne cewa PDP na nan daram a Katsina.” Inji Uche Secondus.

Share.

game da Author