Wani likita da ke aiki a asibitin De-Vine a Abuja, Dapo Morawo ya bayyana wa gidan jaridar PREMIUM TIMES irin abincin da ya kamaci mai dauke da cutar kanjamau ya dinga ci.
Morawo yace cutar kanjamau cuta ce dake karya garkuwar jikin mutum sannan idan mutum na shan magugunan cutar kamata ya yi a hada da wasu abinci domin bunkasa garkuwan jikinsa.
Ga abincin
1. A ci abincin dake dauke da sinadarin ‘Carbonhydrates’ kamar su doya, dankali, masara, buredi da sauran su domin suna taimaka wa jikin mutum da karfi.
2. Abincin dake dauke da sinadarin ‘Proteins’ kamar su wake, kwai,madara da sauran su domin suna tamakawa wajen gina jikin mutum.
3. Cin abincin dake dauke da sinadarin ‘Fats and Oils’ domin hana mutum rama irin wannan abincin sun hada da fiya, kwai, man shanu,kwakwa da man kwakwa, kifi da sauran su.
4. Cin kayan lambu da ganyayyakin domin suna kara wa mutum jini a jiki.