Jami’in da ke kula da Babban Birnin Tarayya Abuja, Umar Shuaibu, ya bayyana cewa gundumar, AMAC, ta kammala shirye-shiryen kakkabe gidajen holewa da wuraren shakatawa masu cika wa jama’a kunnuwa da kade-kade su na hana makwabta barci mai nauyi a cikin dare.
Shuaibu ya ce duk wani wurin shakatawa ko gidan holewa da dare wanda ke cikin unguwannin da gidajen kwana su ke, to za a rusa su.
Ya yi wannan bayani ne a wani jawabi da yi a lokacin da ya ke ganawa da taron manema labarai a karshen makon nan, a Abuja.
Ya ce Gundumar AMAC ta damu kwarai da koke-koken da jama’a ke yi dangane da yadda wasu gidajen holewa da wuraren shakatawa ke cika su da surutai da hayaniya da kuma kade-kade sun a hana su barci.
Shuaibu ya ce sun saurari korafe-kprafen inda suka gano cewa babu makawa, hanya daya da za a hana takura wa mazauna ko masu makwautaka da irin wadannan gidajen rakkashewa da dare, to su ne a dauke su daga cikin jama’a ko unguwannin da gidajen kwana su ke.
Ya kara da cewa, sun kuma lura, baya ga cika wa jama’a kunnuwa da karar lasifika wadannan gidajen holewa da wuraren hutawa da dare su na haddasa cinkoson motoci da dare, ta yadda su ke ajiye motoci a kan titi.
Tuni dai aka fara rushe wasu wurare, yayin da Shuaibu ya kara nanata cewa dokar FCT ta nuna cewa ba a yarda a mallaka maka fili ka gina gidajen holewa a tsakiyar jama’a ba.
Binciken PREMIUM TIMES Hausa ya tabbatar da cewa dubban mazauna garin Abuja da kewaye, musamman mazan su, kan fita yawon shakatawa a gidajen holewa ko wuraren shakatawa musamman gidajen rawa ko na shan barasa, tun daga karfe 9 na dare, wasu su zauna kan tenurin shan barasa har garin Allah ya waye.
Ko da yake da dama na komawa gida da misalin karfe 2 ko uku na dare.
Idan ana maganar kasuwanci a Abuja, to za a iya cewa giya na daya daga cikin kayan shaye-shayen da ake ciniki, domin dukkan gidajen holewar da wuraren shakatawar da akasari kabilun kudancin kasar nan ne suka mallake su, to giya ce aka fi saye a cikin su.
Akwai daidaikun wuraren sayar da kwalama da makulashe ko abinci, irin su Yahuza Suya, wadanda nama ne kadai da lemu za ka saya ka zauna ka ci ko kuma ka dauka ka tafi da shi gida. Ire-iren wadannan wurare kuwa, na kowa ne kabila ne, kowa zuwa ya ke yi, ba kamar gidajen holewa ba.
Wani abin da PREMIUM TIMES Hausa ta kara fahimta shi ne, yawan munanan hadurran da ake yi a cikin birnin Abuja a tsakiyar talatainin dare, masu fitowa ne a sukwane daga gidajen holewa ke haddasa shi, kuma su ne abin ya fi shafa, sai kuma wanda suka gabza wa motar.
Sau da yawa wasu a buge su kan tuko mota a guje, wasu kuma tseren gudun-famfalaki su ke yi idan sun taso daga gidajen holewar, ga su kuma a buge da barasa, wanda hakan ya sha haddasa hadurra da yawa a cikin Abuja.
Ambaliyar gidajen holewa a Abuja da kananan garuruwan da ke kewaye da birnin na daya daga cikin dalilan gurbacewar tarbiyyar yara kanana. Da yake sauran kabilu sun rigaya sun yi kaka-gida a birnin da kuma yankunan garuruwan da ke kewaye da Abuja, akasarin su rayuwar su ba ta da bambanci da rayuwar gidajen holewar.
Discussion about this post