Dakarun sojin sama tare da hadin guiwar dakarun kasa sun sami dakile wasu ‘yan kunan bakin wake dake kokarin tada bam a cikin jami’ar Maiduguri a ranar Lahadi da yamma.
Jami’in yada labaran rundunar sojin sama Olatokunbo Adesanya ya sanar da haka a taron manema labarai ranar Litini a Abuja.
“Tun da muka hango su daga nesa suna kokarin shiga jami’ar Maiduguri sai muka gaggauta far musu. Sai dai kafin mu kai gare su, jigidar bam din daya daga cikin su ya tashi sai hakan ya sa sauran suka tarwatse, wato suka falla da gudu.”
Adesanya yace dakarun sa sun fantsam domin gano maboyar sauran ‘yan kunar bakin waken da suka gudu.