TA ZARCEN BUHARI: ‘Yan Najeriya sun yaba, wasu sun koka

0

‘Yan Najeriya da dama na ta tofa labarkacin bakin su kan tazarcen shugaban Kasa Muhammadu Buhari.

Idan ba a manta ba a safiyar Litinin ne Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya bayyana ra’ayin sa na sake yin takarar shugabancin Najeriya a 2019.

Fadin haka ke da wuya, ‘yan Najeriya kuwa suka farwa shafunan su na sada zumunta da sauran kafafen yada labarai suna fadin albarkacin bakin su kan haka.

Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Balarabe Musa, cewa yayi wannan furci na Buhari bai bashi tsoro ba domin kuwa shima jam’iyyar sa ta PRP za ta fidda dan takarar shugaban kasa a zaben 2019.

Shiko Sanata Ahmed Makarfi cewa yayi wannan furuci na shugaba Buhari bai basu mamaki ba,” Dama cewa yayi ba zai yi takara ba shine zamu cika da mamaki.”

Sakataren jam’iyyar PDP a jihar Sokoto Kabiru Aliyu, cewa yayi lallai fa ‘yan Najeriya su yi shirin fadawa cikin wata sabuwar matsanancin yunwan na tsawon shekaru hudu.

Shiko Kasimu Ciyawa daga jihar Sokoto cewa yayi a shirye suke su ci gaba da mara wa shugaban kasa baya domin ya sake zarce wa a 2019.

” Mun amince da yadda ya ke mulkin Najeriya, kuma za mu ci gaba da mara masa baya.

Shima Sarkin Samarin Barnawa, Kaduna, AbdulAziz Mukhar, a nashi tsokacin ya yabi wannan furuci na Shugaba Muhammadu Buhari.

” Mu Buhari na mu ne kuma muna tare da shi 100 bisa 100. Matasa na tare da shi kuma idan zabe ya zo tabbas shi za mu yi.

” Abin da Buhari yayi wa kasa Najeriya, abu ne da dole mu yaba masa. Samun dama a karo na biyu zai ba shi damar kammala abubuwan da gwamnatin ta fara shekaru hudu da suka wuce.

Sarkin Samari, ya yi kira ga ‘yan Najeriya da su mai da hankali wajen ganin ba ayi amfani da su ba wajen tada zaune tsaye a kasa baki daya.

Share.

game da Author