Kudin siyan makaman Naira Biliyan 360: Sanatoci sun harzuka da Buhari-Saraki

0

Shugaban Majalisar Dattawa Sanata Bukola Saraki, ya bayyana cewa sanatocin kasar nan sun nuna kakkausar rashin amincewa dangane da yadda Shugaba Muhammdu Buhari ya sa hannun kamfatar makudan kudade har naira biliyan 360 domin a sake sayen makamai.

“ Kwanan baya mun ji yadda batun sayen makamai ya sake tasowa a cikin kafafen yada labarai. Amma a cikin gwamnatin da ta san abin da ya kamata, to kamata ya yi kafin a fito da wannan batu a fili, sai an tuntubi majalisar tarayya tukunna. Domin tuni wannan azarbabi da aka yi ya harzuka wasu sanatoci da yawan gaske.” Inji Saraki.

Tuni dai wasu sanatoci biyu da su ka zanta Da PREMIUM TIMES suka ce a gaskiya ba su ji dadin abin da Buhari ya yi ba, kuma sun ce su da wasu ministoci da dama su na bayan Sanata Bukola Saraki.

Idan ba a manta ba, Ministan Tsaro Mansir Dan’Ali ne ya bayyana wa manema labarai a Fadar Shugaban Kasa a ranar Laraba cewa Buhari ya sa hannun amincewa a sayo makamai na naira biliyan daya.

Wannan furuci ya dadada wa wasu magoya bayan shugaban kasa, yayin da wasu kuma ke korafin cewa don me za a kwashi kudade a sayo makamai, tunda yanzu gwamnatin Buhari ta koma zaman sulhu da yin yarjeniya da Boko Haram, har sun a shiga gari su maida wadanda su ka yi garfkuwa da su, bayan sun gana da gwamnati?

Masu sukar gwamnati irin su Ayo Fayose gwamnan Ekiti, tsalle ya yi ya tuma gefe daya ya ce bai aince da cire naira biliyan 360, kwatankwacin dala bilyan daya don a sayo makamai ba, domin kawai wayau ne da nufin a karkatar da kudaden saboda zaben 2019 kawai.

Share.

game da Author