Dakarun soji sun kora Boko Haram a Gamboru Ngala

0

Jami’in rundunar sojin Najeriya Texas Chukwu ya bayyana cewa rundunar sojin ‘Operation Lafiya Dole’ sun sami nasaran kora wasu ‘yan Boko Haran daga kauyen Gamboru-Ngala dake jihar Borno.

Ya sanar da haka ne ranar Asabar a Maiduguri.

Chukwu ya bayyana cewa sun yi arangama da ‘yan Boko Haram wanda sanadiyyar haka suka kashe daya daga cikin ‘yan Boko Haram din sannan sauran suka gudu.

” A arangamar da muka yi da su muma mun rasa soja daya.”

A karshe Chukwu ya ce sun kwato makamai da dama da Boko Haram suka gudu suka bari bayan dakarun sun fatattake su.

Share.

game da Author