Sanata mai wakiltar Kaduna ta tsakiya ya mika sakon jajen sa ga hukumar Zabe ta jihar Kaduna bayan gobara da ya lashe ofisoshin hukumar a safiyar Asabar.
Sanata Shehu Sani, ya mika sakon jajen sa sannan ya yi kira ga hukumomin tsaro da na hukumar Zaben da su gudanar da bincike don gano musabbabin wannan gobara ganin cewa anan gab da gudanar da zaben kananan hukumomi a jihar.
Mai ba sanata Shehu shawara kan harkar yada labarai Abdussamad Amadi da ya fidda wanna sako in da sanatan ya kara da cewa yana fatan wannan gobara ba zai hana zaben kananan hukomomi dake tafe.
A karshe sanata Shehu ya gode wa wa Allah ganin cewa gobarar bata ci rai ko daya ba kuma ba a sami rahoton wani ya sami rauni ba. Sannan kuma ya jinjina wa ‘yan unguwa da suka taimaka aka kashe wutar.