Kungiyar ma’aikatan jinya JOHESU ta lashi takobin ci gaba da yajin aikin da ta fara a makon da ya gabata, cewa barazanar da gwamnati take yi cewa baza ta biya ma’aikatan kungiyar albashi ba, ba zai tsorata ta mambobin kungiyar ba.
Gwamnatin tarayya ta yi wa kungiyar JOHESU barazanar cewa zata dakatar da ci gaba da biyan su albashi muddun basu janye yajin aikin ba.
A tsokacin da ya yi ranar Juma’a shugaban kungiyar Biobelemoye Josiah ya bayyana cewa ‘‘Muna so mutanen kasar nan su fahimci irin rashin nuna adalci da nuna wariya da shugabanin ma’aikatar kiwon lafiya ke yi mana da likitoci sannan duk da haka gwamnati ta na mara musu baya domin har barazana take yi mana na hana mu albashin mu idan ba mu dakatar da yajin aikin ba.
A karshe Josiah ya roki gwamnati da ta karkato da akalarta zuwa ga abin da ya dace tayi ba biye wa wasu da ba su kaunar ci gaban fannin Kiwon Lafiya na Kasar nan.