ZUWAN BUHARI JOS: An tura karin ‘yan sanda sama da 2000

0

Jami’in harka da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Filato Terna Tyopev ya bayyana cewa sun aika da ‘yan sanda 2,435 da za su samar da tsaro yayin da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ziyarci jihar.

Ya sanar da haka ne ranar Alhamis a lokacin da yake hira da PREMIUM TIMES ta waya inda ya kara da cewa yin haka ya zama musu dole musamman ganin yadda rikici ya barke a kauyen Daffo dake karamar hukumar Bokkos a daren Laraba.

Tyopev yace a dalilin wannan hargitsi da aka yi mutane biyar wanda duk mata ne sun sami rauni a jikin su.

Ya ce an kai su asibitin Jos domin samun kula.

Share.

game da Author