Shugaban hukumar kwastam dake kula da shiyar Sokoto, Kebbi da Zamfara Nasir Ahmed ya bayyana cewa sun kama tankin man fetir da aka boye jarkunan man gyada wanda gwamnati ta hana shigowa da su.
Ahmed ya sanar da haka ne da yake zantawa da manema labarai a Sokoto inda ya kara da cewa sun tsamo jarkunan man gyada 446 daga cikin wannan tankin mai a hanyar Sokota zuwa Gusau.
” An kiyasta kudin su zai kai Naira miliyan 5.7.”
Ya yi kira ga mutane da su hada kai da ma’aikatan hukumar don ganin an kau da masu fasakwauri a iyakokin jihar.
Discussion about this post