Kashi 20 na yaran da suka kammala firamare a Najeriya ke iya karatu -Bankin Duniya

0

Wani sabon rahoton da Bankin Duniya ya fitar, ya bayyana cewa kashi 20 cikin 100 ne kadai na daliban da suka kammala firamare, ke iya karatu a Najeriya.

Rahoton Bankin Duniya na 2018, an kaddamar da shi ne tare da hadin-guiwar Ma’aikatar Kudi ta Tarayya da kuma Ma’aikatar Ilmi a ranar Talata.

Daga nan sai rahoton ya yi kira da a dauki kwararan matakai da kuma karin ingantaccen tsari.

Rahoton ya ce gudanar da tsarin ilimi wanda dalibai ba su fahimta, kuma wanda ba ya samar da hazikan yara, to asarar dukiya ce kuma zalinci ne ga yara kanana da kuma tauye musu bakki.

Share.

game da Author