RIKICIN FILATO: An kama wani makiyayi dauke da bindiga

0

Rundunar ‘Yan sandan jihar Filato ta sanar cewa akalla mutane 16 ne suka rasu a rikicin da aka yi daga ranar 7 zuwa 9 ga watan Maris a wasu kauyukan karamar hukumar Bokkos.

Idan ba a manta ba a makon da ta gabata ne PREMIUM TIMES ta rawaito cewa wasu mahara sun kai hari a kauyen Nzharuvo dake karamar hukumar Bokkos.

Wani shugaban matasan kauyen mai suna Danjuma Auta ya bayyana wa PREMIUM TIMES cewa maharan sun far wa mata ne da yara kanana a kauyen.

Duk da haka mazaunan karamar hukumar sun bayyana wa manema labarai ranar Lahadi cewa mutane 25 ne suka rasa rayukansu sanadiyyar wannan rikicin.

Mazaunan sun kuma kara da cewa suna zargin makwabtansu Fulani ne suka far musu a kauyukan Nghakudung, Shilim, Morok, Mandung, Faram, Filla, Hotom, Dai, Kungul, Hurum, Dahua, Malul, Warrem, Josho da Ganda.

” Sanadiyyar wannan rikicin mutane 5,000 sun rikida sun koma ‘yan gudun hijira.”

A karshe jami’in harka da jama’a na rundunar Terna Tyopev ya ce yayin da suke gudanar da aikin tsaro a kauyen Daffo jami’an su sun kama wani makiyayi mai suna Muhammadu Bimini dauke da makami.

Share.

game da Author