Darektan kamfen din jam’iyyar APC a jihar Akwa-Ibom a 2015, Soni Udom, ya ce da ya ci gaba da zama a jam’iyyar APC ya gwammmace ya koma PDP da in soyewa za suyi duk su soye a can.
Udom ya kara da cewa ” Duk wahalar da nayi wa jam’iyyar APC a 2015, ba ta haifar min da komai ba face wahala da takaici. An yi watsi da mu kamar ba a san mu ba, wasu ne can ko shan romon gwamntin.
” Ya fi min in koma PDP, idan soyewa za muyi mu ma babbake a can duk na san ba haka bane, ita lema inuwa ake sha, ita kuma zan sha.
Sanata Godwill Akpabio da wasu jigajigan jam’iyyar PDP ne a jihar Akwa-ibom suka karbi Udom sannan suka yi masa lale- lale barka da dawowa.