KIWON LAFIYA: Ana rasa yara 756,000 ‘yan kasa da shekara biyar a Najeriya duk shekara

0

Babban sakataren ma’aikatar kiwon lafiya Osarenoma Uwaifo ya bayyana cewa a wani binciken Hukumar majalisar dinkin Duniya na ‘UN Inter-agency Group for Child Mortality Estimation (ICCM)’ ya nuna cewa duk shekara yara 756,000 ‘yan kasa da shekara biyar na rasa rayukan su a Najeriya.

Ya fadi haka ne a taron samun madafa don inganta kiwon lafiyar yara kanana a kasar wanda aka yi a babban Birnin tarayya, Abuja.

Uwaifo ya ce binciken ya kara nuna cewa Najeriya ce ta biya a jerin kasashen da ke fama da wannan matsalar a duniya.

Ya ce sanadiyyar rashin kawar da cututtuka kamar su amai da gudawa,cutar sanyi dake kama hakarkari da yunwa ne ke hallaka yara.

Uwaifo yace Najeriya za ta iya kawar da wannan matsaloli ne idan ta inganta kiwon lafiyar kasar nan ta inda yara kanana za su na samun kula ta musamman.

Share.

game da Author