Ko a daina kashe mutanen mu a Taraba, ko kuma sai an ce yakin Somalia wasan yara ne a kasar nan – Inji Theophilus Danjuma

0

Tsohon ministan tsaro, Theophilus Danjuma ya koka kan yadda dakarun soji ke taimakawa wajen rura wutan ayyukan ta da zaune tsaye da ake fama dashi musamman a jihar Taraba, da sauran kauyukan jihar da ma kasa baki daya.

Danjuma ya bayyana haka ne a wajen taron bukin yaye daliban jami’ar Jihar Taraba dake Jalingo.

” Dole ne a dai na kashe kabilun mu a jihar Taraba ko kuwa sai an ce yakin da akayi fama dashi a kasar Somalia wasan yara ne.

” Kowa ya tashi tsaye yayi shirin kare kan sa. Kada ya ce zai jira sojin Najeriya suyi masa haka. Domin idan kuka ce za ku tsaya wai a samar muku da kariya, za a ko kashe ku daya bayan daya kuna ji kuna gani.

Danjuma ya furta cewa mai makon jami’an tsaro su kare jama’a sune suke taimaka musu suna yi musu shinge domin su kai wa mutane hari. Ya ce idan har ba a dauki mataki cikin gaggawa ba Najeriya za ta tarwatse.

Da muka ne ji daga bakin Kakakin ma’aikatar tsaron Kasa, John Agim ya bayyana mana cewa duk da soji na ganin girman Danjuma a matsayin sa na tsohon Dakare, ba za ta yarda da abin da yake fadi ba.

” Sojin Najeriya na da kwarewa ta musamman, ba za su yi irin abin da Danjuma ke fadi. Ya dai fadi albarkacin bakin sa ne kawai. Sojin Najeriya ai wuce nan.”

Share.

game da Author