Daya daga cikin daliban da aka sace daga makarantar #Dapchi, mai suna Khadija Grema, ta zanta da ‘yan jarida, inda ta bayyana abubuwan da suka faru da su tun bayan da Boko Haram suka sace su a ranar 19 Ga Fabrairu, 2018.
Khadija, wadda ke sanye da wani zumbulelen hijabin da Boko Haram suka dunka wa dukkanin su, ta kuma bayyana yadda wasu daliban suka rasa rayukan su bayan sace sun da ka yi.
“A ranar da abin ya faru, mu na cikin makaranta, mu na shirin yin buda-bakin azumin ranar Litinin da mu kan yi, sai muka gan su sun shigo. Dukkanin mu muka gigice, aka fara kuka. Daya daga cikin su ya ce mu zo wurin sa. Suka fara harbi a sama, gaba daya muka firgice. Muka runtuma a guje zuwa bakin kofar makaranta. (Premium Times Hausa)
“Lokacin da muka isa bakin kofa, sai suka kira wani Babangida, suka ce ya je ya kawo motocin da za a dauke mu. Aka kawo motoci, suka sa mu ciki, daga nan aka fara fita daga kusa da Dapchi. (Premium Times Hausa) Bayan mun fita gari, sai suka tambaye mu a cikin mu su wa da wa ke yin azumi ne? suka ce dukkan masu azumi su sauko. Suka ba masu azumi Maltina, nama, gyada, cake da ruwan leda.
“Bayan mun yi buda-baki, sai muka yi sallah, daga nan kuma muka ci gaba da tafiya har muka kai inda wata babbar itaciya ta ke. Muka yada zango a nan. Aka ce mu sauka mu dafa abinci. A lokacin dare ya riga ya yi, sai suka kunna fitillu.
“Bayan mun gama cin abinci, sai muka ci gaba da tafiya, har muka kai inda wata korama ta ke. Daga nan sai aka ce duk mu fito mu shiga kwale-kwale. Muka yi ta shiga kwale-kwale ana tsallakar da mu.
“A can tsallaken sai suka kai mu cikin wani gida a wani kauye, wanda ban san ko ina ba ne. A can suka ajiye mu.
Washegari kuma suka sake daukar mu a ciki kwale-kwale muka ci gaba da tafiya, har dai muka kai cikin wani daji mai surkuki, suka ajiye mu a can kuma ba su sake canja mana wuri ba.
“Su na ciyar da mu sosai, ba su bar mu da yunwa ba. Ba wadda aka doka, kuma babu wadda aka tozarta wa mutunci.
“Mutanen da suka gudu da mu dukkan su da yaren Kanuri da Larabci su ke magana. (Premium Times Hausa) Kuma ba su fada mana wani dalilin da ya sa suka dawo da mu ba. Sun dai ce mana kawai sun ga mu musulmai ne, ya kamata su sake mu, don kada mu sha wahala.”
Ta ce wasu daga cikin yaran da aka sace din kanana ne kwarai, su ne aka tattake a lokacin da aka kwashe su da mota aka gudu da su daga Dapchi.
“Yara biyar suka mutu a lokacin da ake fita da mu daga Dapchi bayan mun shiga daji. A cikin motoci aka tattake su, saboda cinkoso.” Inji Khadija.
“Babu wanda ya taba mu ko ya yi lalata da mu. Sun ce ma bai dace namiji da mace suna zama a wuri daya ba.
LEAH SHERABU: Yarinyar da ba a sako ba
Khadija ta ce an yi musu albishir da alkawari cewa duk za a sake su a maida su gida, amma banda yarinya daya, Leah Sherubu, wadda Kirista ce kuma ta ki yarda ta rika saka hijabi, ko kuma ta karbi musulunci.
Bukar ya ce ba su ji dadin rashin sakin Leah ba. Kuma ya sosa musu rai matuka.
Iyayen daliaban Chibok a Dapchi
A lokacin da aka maida daliban Dapchi gida, iyayen daliban Chibok su na garin. Har yanzu Boko Haram na rike da dalibai na Chibok sama da 100, TUN 2014, wadanda ba su kammala saki ba.
Sun isa Dapchi ne a ranar Talata domin su taya iyayen daliban Dapchi jimamin kuncin irin halin da su ma suka tsinci kan su a ciki.
Su kuma ‘yan jaridar da suka je garin a ranar Laraba, ba su da masaniyar batun sakin daliban Dapchi, sun je ne a bisa gayyatar iyayen daliban Dapchi suka yi musu domin su dauki rahoton ganawar da za su yi da iyayen daliban Chibok da suka kai musu ziyarar jaje.