Mai unguwar kauyen Fagam dake karamar hukumar Gwaram jihar Jigawa ya kori umarci wasu Fulani da su tattara nasu-ina-su su fice daga wannan kauye tun da wuri.
Daya daga cikin mazaunan rugar da mai unguwar ya umurta da su tashi, Shehu Juli ya bayyana wa PREMIUM TIMES cewa ya basu wata daya ne cur su tashi ko su gamu da fushin sa.
” Sai da suka jira mahaifina ya rasu sannan suka ta da wannan magana na tashi barin wannan kauye.
” Ko da yake da muke zaman juyayin rasuwar mahaifina dakace Adamu ya turo wasu mutane da suka bani wani takarda da bansa ko menene aka rubuta ba na sa hannu a kai.”
” Yanzu da aka ce mu tashi daga wannan ruga ina ake so mu koma?”
Ita kuwa mahaifiyar Juli mai suna Ladi ta fadi wa gidan jaridar cewa sun yi sama da shekaru 40 a rugan suna tare da dabobinsu da kuma manoman kauyen lafiya lau, rasuwar, ” Allah na dauke mijina sai mai unguwar ya bujiro da wannan maganar tashin hankali.”
” Ba mu da wurin da za mu koma sannan gashi kayan abincin mu sun kusa karewa.”
Ta ce abin da ya fi bata mamaki shine yadda wani babban aminin mai gidanta ya ki tausaya musu inda shi da kan sa ya rako masu kawo mana takardar tashi daga wannan ruga da muka zama.
Da PREMIUM TIMES nemi ji daga bakin mai unguwan wannnan kauye Auwalu Adamu, sai ya shaida mana cewa su yi hakane ganin cewa wadannan makiyaya basu biyan haraji da ladan zama a wannan ruga.
” Kowa ya san cewa dole ne a biya wannan haraji wanda shi mahaifin su bai taba fashi ba.”
Shugaban kungiyar makiyaya na Miyetti Allah reshen jihar Jigawa Sa’adu Musa Gagarawa ya gargadi wannan mai unguwa da ya janye wannan takarda tasa cewa bashi da ikon korar wasu mazauna wannan kauye sannan yayi kira ga sarkin Dutse da gwamnatin jihar da su saka bai kan wannan magana.