AN KI CIN BIRI AN CI DILA: Mu na biyan naira miliyan 774 a kowace rana, tallafin rarar mai – NNPC

0

Kamfanin mai na kasa, NNPC ya bayyana cewa a kowace rana ya na asarar naira miliyan 774 a matsayin kudaden da ya ke cika wa masu sayen fetur, sanadiyyar karin amfanin da man da ake yi a kasar nan.

Wannan kifadi da NNPC ke yi, ta jajirce cewa ta na cika kudin ne, domin kawai ta tabbatar an sayi mai a kan naira 145 kowace lita, duk kuwa da cewa ya zarce hakan. Sai dai kuma kiri-kiri NNPC ta ki fitowa fili ta ce ta na biyan kudin sassaucin farashin fetur, wato ‘subsidy.’

NNPC ta lura cewa yawan amfani da fetur ya karu da lita milyan 50 a kowace rana, dalili kenan ta ke kara asarar wajen cike rarar farashin kowace lita.

Wadannan kudade da ta ke cikawa, sun kunshi cikon kudaden tashin farashin saukalen fetur da NNPC ke sayowa daga kasashen waje da kuma farashin da ta ke saida wa masu gidajen mai.

NNPC ta ce ita ma ta na cike gurbin kuden da ta ke kashewa ne ta hanyar cire su daga kudaden shigar da ta ke tara wa gwamnatin tarayya.

A baya dai NNPC ya sha cewa lita daya ta main a kama mata naira 171 ne.

Kakanin NNPC, Ndu Ughamadu ne ya bayyana haka tare da cewa shugaban hukumar NNPC din ne, Maikanti Baru ya bayyana haka kwanan nan.

Baru ya ce an samu yawaita giggina gidajen mai kwanan nan a fadin kasar nan, sannan kuma masu sumogal din fetur zuwa kasashen ketare su na cin karen su babu babbaka.

Ya ci gaba da cewa gyaran yadda za a rika raba man a kasar nan na neman ya gagara saboda wadannan matsaloli.

Da ya jagoranci tawagar NNPC zuwa wata ziyara ga shugaban kwastan na kasa, Hamid Ali, Baru ya yi kira da a samu hadin-guiwa tsatsanin hukumar kwastan da NNPC yadda za a magance masu fasa-kwaurin fetur daga cikin Nijeriya zuwa kasashen da ke makwautaka da ita.

Share.

game da Author