PREMIUM TIMES Hausa ta yi tsakure daga cikin doguwar tattaunawar da Mataimakin Shugaban Kasa, Yemi Osinbajo ya yi da kafafen yada labarai a Legas.
Batun ikirarin yawaitar cin hanci da rashawa da kungiyar Transparency International ta fitar
OSINBAJO: To wannan dai sai da suka yi kididdiga, ba kirdado suka yi ba. Sai mu yi nazari mu gani, a cikin kididdoga 9 da suka yi a baya, a cikin guda 9 din nan, sun ce mun gusa gaba a cikin guda 4, mun yi tsaye cak a cikin kididdiga hudu, yayin da muka ci baya a cikin kididdiga daya tal.
To kun ga kenan abu mafi muhimmaci da al’ummar kasar nan za su gane shi ne, yadda gwamnati ta yi wa rashawa daukar daki, irin wanda ba mu taba ma gani ba a baya. Misali, an ragargaza dala biliyan 15 a fannin kwangilar makamai, an sungume naira bilyan 100 cif ana saura sati biyu a yi zabe, aka sake daka wa wata dala milyan 293 wasoso makonni uku a yi zabe. Ga kuma badakalar da aka tabka a NNPC.
Ashe za ku gane cewa abin ba karamar managa ko karamin aiki ba ne. To wadannan su ne sagwangwamai da somin-tabin durkushewar tattalin arzikin kasar nan ai.
Su wane ne hukumomin da ake bin matakan yaki da cin hanci da rashawa da su?
OSINBAJO: Abin ai tsari ne na musamman, amma ba wata hukuma ba ce ita kadan kacal ke aikin. Yin abu online wata hanya ce. Ga tsarin asusun ajiyar bai-daya na TSA. Ga kuma EFCC wadda ake bari ta yi aikin ta babu mai sa mata baki.
Wane tsari ake bi na kasa bai-daya wajen yaki da cin hanci da rashawa?
OSINBAJO: Wannan kuma wata doguwar magana ce daban. Amma a takaice dai hanya ko tsarin da ake bi shi ne mu na tabbatar da cewa musamman ma’aikatan gwamnati ba su samun damar duma hannu su a kan dukiyar gwamnati ko na ce dukiyar al’umma.
Muna bin wannan tsari ne tare da tabbatar musu da cewa duk wanda ya ci nanin, to sai nanin ta ci shi.
Banda EFCC, mun ga kamar akwai wata hukuma mai yaki da cin hanci da rashawa, misali ICPC, amma su ba su tabuka komai.
OSINBAJO: Ban fa yarda a ce irin su ICPC ba su yin aikin komai ba. Mun inganta hukumar, mun kafa mata majalisar mashawarta, kuma ta na ciki tsundun wajen yaki da cin hanci da rashawa. Mun karfafa shugabannin hukumar, amma abin takaici abubuwa sun yi cak a hukumar saboda mun yi zaune mu na jiran Majalisar Dattawa ta rattaba hannun amincewa.
‘Yan Najeriya mazauna kasashen waje na daya daga cikin masu sama wa kasar nan kudaden musaya na kasar waje. An ce su kan samar da kamar dala bilyan 20. To ko Najeriya na da wani shiri da take yi na hadin guiwa da ‘yan Najeriya mazauna kasashen waje?
OSINBAJO: Ai tsakanin mu da su ya ma wuce kafa ofishin mai bada shawara akan ‘yan Nijeriya mazauna kasashen waje kawai. Mu na bukatar su wajen inganta fasaha, kimiyya, tallalin arziki, kiwon lafiya da saura da dama, kuma duk abin da ya kama a yi da su, to da su din ake yi.
Ana zargin Shugaba Buhari na nuna bangaranci, kabilanci, ’iyan’uwanci ko shiyyanci.
OSINBAJO: Wannan duk surutai ne kawai. Ka kalli ministoci, idan ka kawo maganar addini, to daidai da daidai ake, Musulmi na da 18, Kiristoci na da 18. Amma Sakataren Gwamnatin Tarayya da Shugaban Ma’aikata duk Kiristoci ne. to kenan muna da Kiristoci 20 Musulmi 18 a cikin Majalisar Zartaswa kenan.
Ga kuma wani misali, Jihohin Kudu-maso Gabas sub biyar ne, amma jihohi hudu daga cikin su na da manyan ministoci, ai daya ce ta ke da karamin minista. Amma ka dubi sauran jihohin Arewa ka gani.
Ai a nan shugaban kasa ba shi da yadda zai yi, domin dokar kasa ce ta ce tilas sai an dauko daga ko’ina.
OSINBAJO: Shugaba na da cikakken iko a wajen nada mukamai da ministoci. Jihohi bakwai na Arewa, har da Katsina, jihar da shugaban yake ba su da babban minista, duk karamin minista su ke da shi.
Batun inganta darajar ilmi.
OSINBAJO: Akwai hanyoyi da yawa da ake kai wajen farfado da darajar ilmi a kasar nan. Idan za ku tuna a farkon Janairu mun yi taron sanin-makamar gyara ko farfado da fannin ilmi. Akwai shirye-shirye da dama, kamar daukar malamai na tsarin N-Power, inganta fasaha, bayar da horo ga wadanda suke da digiri da sauran tsare-tsare da dama. Kun san kuma shi fanninn ilmi fadi gare shi sosai, ba a ilmin firamare ko sakan dare kawai ya tsaya ba.
Kasafin kudi na 2018 dai shiru ake ji har yanzu.
OSINBAJO: Kun san dimokradiyya mu ke bi, ita ce tsarin mulkin mu. To mu na da bangaren gudanar da mulki har gida uku. Tilas sai Majalisar Dattawa da ta Tarayya sun duba kasafin tukunna.
Kuma idan za ku iya tunawa, ai ni ne na sanya wa kasafin 2017 hannu. Da na ke jawabi na ce aiki da kasafi daga Janairu 2018, zai rika farawa ne daga Janairu zuwa Disamba. Yanzu dai mu majalisa kawai muke jira. Su ne suka hana mu yin katabus.
Sabani ko rashin fahimta tsakanin bangaren Gwamnati da Majalisar Tarayya
OSINBAJO: To ni dai ban tabbatar akwai wani sabani da ya ke a boye tsakanin gwamnati da MajalisarTarayya ba. Domin ko a Amurka inda mu ka aro na mu tasrin mulki, sai an bi matakai kafin a zartas da abubuwa. Ko ma dai me ke nan, ya kamata a sani cewa duk abin da gwamnati za ta yi to wajibin majalisa ne ta bi diddigi ta gane yadda abin ya ke dalla-dalla kafin ta mince tukunna.
Ya aka yi gwamnatin ku ta gaji bashin naira tiriliyan 9, amma ita kuma cikin shekaru biyu da rabi ta ramto naira tiriliyan 30? Ya aka yi haka?
OSINBAJO: A’a, a’a, ko kadan ba na jin haka abin ya ke. Zan shaida muku cewa gwanatinmu na da tsentseni, bin-diddigi, matsolanci da kuma yin abu keke-da-keke. A karon farko a tarihin kasar nan, gwamnatin mu ce za ta fara kashe naira tiriliyan daya da digo uku, bilyan 1.3 a kan manyan ayyuka.
Ni ina ganin abin dubawa shi ne idan an ce wata gwamnati ta ramto naira tiriliyan 9, sai a duba a ga wane aiki ta yi da tiriliyan 9 din nan. Sannan a wancan lokacin kuma har dala 115 aka rika saida gangar danyen mai, sabanin yanzu da farshin fetur din ya fadi warwas.
An ce kashi 50 bisa 100 na kudaden shigar kasar nan, duk a biyan bashi ya ke tafiya?
OSINBAJI: Ba gaskiya ba ne, abin da kenan shi ne, a yanzu mu na da jbin kusan naira tiriliyan 2.6. mun fi bada karfi wajen kashe kudade kan manyan ayyuka da kuma biyan ma’aikata. Maganar gaskiya ita ce mu mana so mu rika gudanar da ababen more rayuwa da za su dade ana morar su.
Me ya sa duk da kashe-kashe a Benuwai, Zamfara, Taraba da sace daliban Dapchi, Shugaban Kasa bai kai ziyara can ba?
OSINBAJO: Wato zan iya cewa babu wata za’aziyya ko tsananin jaje da zai iya dawo da rayukan da suka salwanta ko a Benuwai ko Taraba ko Zamfara, kai ko ma ina ne. A nawa bangaren na je Benuwai a cikin Satumba, to sai kuma ga abin da ya faru a Dapchi. Babbar magana a nan ita ce tabbatar da tsaro a wadannan wurare. Mu na bakin kokari wajen tura jami’an tsaro a wurare badan-daban.
Duk da irin kokarin da ku ke yi, ‘yan Najeriya na bukatar ganin ku a wadannan wurare domin su gan ku, ku taya su kukan mutuwa da kuma jimamin salwantar dukiya.
OSINBAJO: A gaskiya ni ma na yarda da hakan. Idan muka bi muka yi jaje hakan zai fi sosai. Amma abu na gaba shi ne yadda za mu gyara wuraren da aka barnata wa jama’a. Amma zancen gaskiya na yarda da kai, da a ce ni da Shugaban Kasa mun bi wurwren nan mun je jaje, to da abin zai fi tasiri sosai.
Discussion about this post